1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta kira taro kan Iran

Ramatu Garba Baba
July 22, 2019

Theresa May ta kira wani taron gaggawa da ya hada kan manyan jami'an gwamnati dana tsaro, kan takaddamar da ta kunno kai bayan da Iran ta kama tankar man kasar

https://p.dw.com/p/3MUZT
USA Treffen Theresa May und Hassan Rohani
Hoto: Getty Images/C. Furlong

A ranar Jumma'ar da ta gabata ne dai Iran ta kame tankar man Britaniyan a mashigin ruwan Hormuz. An yi ta kace-nace ba tare da an samar da maslaha ba. Ko a ranar Lahadin da ta gabata, Ministan harkokin wajen kasar ta Birtaniya Jeremy Hunt, ya bayyana takaici kan matakin da gwamnatin Teheran ta dauka na nuna halin ko in kula a shawo kan wannan rikicin da ke son janyo wa kasashen biyu tsamin dangantaka. Saboda haka ne  Firaministar Birtaniya Theresa May ta kira wani taron gaggawa da ya hada kan manyan jami'an gwamnati dana tsaro, kan takaddamar da ta kunno kai bayan da Iran ta kama tankar man kasar.