1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta sake neman EU ta jinkirta mata

March 20, 2019

Birtaniya ta sake mika bukata ga shugabannin kungiyar Tarayyar Turai wato EU, na tsawaita mata wa'adin ficewarta daga kungiyar.

https://p.dw.com/p/3FN5v
England, London: Theresa May
Hoto: picture-alliance/AP/M. Duffy

Firaministar kasar Theresa May ta sake mika bukata ga shugabannin kungiyar Tarayyar Turai wato EU, na tsawaita wa'adin ficewar kasarta daga kungiyar zuwa ranar 30 ga watan Yunin bana.

Birtaniya ta mika bukatar a wannan Laraba a Brussels babban birnin kasar Beljiyam, a jajibirin taron kolin da kungiyar da za ta yi. 

Shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk, ya ce ana iya bai wa Birtaniya karin wani takaitaccen lokaci na jinkirta ficewarta daga kungiyar kasashen, bisa sharadin samun goyon bayan majalisar kasar.

A ranar Alhamis ne majalisar Turan za ta tattauana batun daga cikin batutuwan da ke a gabanta lokacin taron na koli.