1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Blaise Compaore ya yi murabus

Pinado Abdu WabaOctober 31, 2014

A yau 31 ga watan Oktoba shekara ta 2014, kasarta Burkina Faso ta kafa tarihi, bayan da adawarsu ta kai ga murabus din shugaban kasar bayan shekaru 27 na mulki.

https://p.dw.com/p/1DfAb
Blaise Compaore Präsident von Burkina Faso Archiv Juli 2014
Hoto: AFP/Getty Images/Sia Kambou

Daga bayanan da kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar, Shugaba Blaise Compaore ya bayyana cewa ya yi murabus a cikin wata sanarwar da ofishin shugaban kasar ya fitar wanda kuma aka karanta a gidan telebijin na kasa, ya kuma kara da cewa yanzu babu kowa kan wannan mukamin. Dama dai tun da farko wani babban hafsan sojin kasar ya fito cikin taron jama'a ya bayyana cewa an hambarar da shugaba Blaise Compaore, abin da ya janyo shewa daga masu zanga-zangar da ke kira da ya yi murabus.

Kanar Boureima Frata ya yi wannan sanarwar ne ga dubban mutanen da suka yi dandazo a gaban shelkwatar sojojin, yana mai cewa daga yau, "Compaore ya daina rike madafun ikon wannan kasar".

Ya kuma yi wannan sanarawar ne da ranar yau yayin da wasu sojojoji ke dauke da shi a kan kafadarsu.

Bayan nan ne kuma Leftanant Kanar Issaac Zida ya sanar da murabus din shugaban a dandalin Place de la Nation idan dubban mutane suka taru.

A yanzu haka dai, wasu rahotanni na cewa an hango wani ayarin motocin da ake kyautata zaton nasa ne, ya nufi wani gari mai suna Po da ke yankin kudancin kasar, da nufin tserewa zuwa Ghana