1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram na ci gaba da yada ta'addanci

Mohammad Nasiru AwalJanuary 2, 2015

Yanzu haka dai ayyukan tarzoma na kungiyar ta Boko Haram sun tsallake kan iyaka zuwa kasar Kamaru makwabciyar Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1EEBJ
Boko Haram Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo

Bari mu fara da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda a wannan mako ta mayar da hankali a kan Boko Haram tana mai cewa.

Kungiyar Boko Haram na yada ayyukan ta'addanci amma sojojin Kamaru sun kare kansu daga hare-haren masu kishin addinin. Yanzu haka dai ayyukan kungiyar ta Boko Haram sun tsallake kan iyaka zuwa kasar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya. Sai dai sojojin kasar sun dakile wani hari da mayakan Boko Haram kimanin mutum 1000 suka kai kan wani sansanin sojin na Kamaru. Jaridar ta ce tun a wasu makonni baya Kamaru ta girke dubun dubatan sojojinta domin tabbatar da tsaro a kan iyakokinta da Najeriya. Amma karancin hadin kai tsakanin dakarun tsaron kasashen biyu na kawo cikas bisa manufa. Ta ce a nata bangaren rundunar sojin Najeriya ta sha ba da rahotannin boge game da samun galaba kan Boko Haram. Jaridar ta ce irin wadannan rahotanni maras sahihanci, sun yi matukar bata sunan shugaba Goodluck Jonathan wanda ke neman yin tazarce a zaben watan Fabrairu. A daya hannun kuma ana zargin sojojin Najeriya ta kai hare-hare da kuma cin zarafin fararen hula.

Jigo a kungiyar al-Shabaab ya mika kai

Har yanzu dai muna kan batun tarzoman, inda jaridar Neue Zürcher Zeitung ta mayar da hankali kan wani jigon kungiyar al-Shabaab da ya mika kai.

AMISOM - Soldaten in Somalia
Hoto: picture alliance/dpa/Jones

Ta ce dakarun gwamnati sun tsare shugaban bangaren leken asiri na kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabaab Zakariya Ismail Ahmed Hersi bayan ya mika kanshi ga dakarun a ranar Asabar da ta makon jiya. Jaridar ta ce Hersi ya kasance babban aminin shugaban al-Shabab Ahmedi Abdi Godane wanda a cikin watan Satumba ya rasa ransa a wani farmaki da jiragen saman Amirka suka kai. Kuma a matsayinsa na jagoran bangaren leke asirin al-Shabaab Hersi ya kasance daya daga cikin 'yan ta'adda da Amirka ke nemansu ruwa a jallo, inda ma gwamnati a Washington ta sanya ladar dala miliyan uku a kan wanda ya ba da rahotannin da za su kai ga cafke shi. Sai dai ba a san ainihin bangaren da Hersi yake ba, bayan al-Shabaab din ta dare gida biyu kuma ba a san karfin ikonsa a cikin kungiyar ba bayan mutuwar Godane. Sai dai jaridar ta rawaito majiyoyin sojin Somaliya na cewa Hersi da kanshi ne ya tuntubi gwamnati kuma ya shiyar yadda za a kama shi.

Rayuwar 'yan jarida na cikin hatsari a Kwango

Karte DR Kongo Nord-Kivu Süd-Kivu Goma Bukavu eng

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan mako ta leka kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ne inda ta labarto kisan da aka yi wa dan jaridar kasar Robert Shamwami Shalubuto wanda aka harbe har lahira a garin Goma da ke gabashin kasar. Ta ce ko da yake babu bayani game da wanda ya aikata wannan ta'asa da kuma dalilinsa, amma wani abokin aikin dan jaridar ya ce tun a bara ne aka yi yunkurin halaka shi. Kuma a baya bayan nan an tsare shi tsawon watanni bayan ya ba da labarin kisan gilla da aka yi a wata unguwar talakawa marasa galihu a garin Goma. Da ma dai rayuwar 'yan jarida a gabashin Kwango tana cikin hatsari, musamman masu kokarin bankado irin aika-aikar da ke faruwa a yankin.