1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram na wahalar da sojin Najeriya

Gazali Abdou Tasawa
January 8, 2019

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince cewa lalle sojin Najeriyar na jin jiki a yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta kaddamar da sabbin hare-haren a yankin Arewa maso gabashin kasar a baya-bayan nan. 

https://p.dw.com/p/3BBtY
Nigeria Notstand Islamisten Truppen Armee Soldaten
Hoto: Reuters

Shugaba Muhammadu Buhari mai shekaru 76 da kuma ke neman sabon wa'adin shugabancin kasar ya karba gazawar sojin kasar tasa ne a wata hira ta musamman da ya yi a yammacin jiya Litinin da tashar talabijin ta Arise TV inda ya amince da cewa salon yakin sari-ka-noke da kungiyar ta Boko Haram lalle ya gajiyar da sojojin kasar da ma haifar masu da damuwa. Sai dai kuma ya ce kasar na kara daukar sabbin matakai na kawar da kungiyar ta Boko Haram. 

A baya dai Shugaba Buhari ya sha ikirarin cewa sojojin Najeriyar sun yi nasarar karya lagon kungiyar ta Boko Haram. To amma sabbin hare-haren da kungiyar ke ta faman kai wa a baya bayan nan musamman a barikokokin sojin kasar ya canza tunanin da shugaban ke da kan wannan yaki. 

Ko a jiya Litinin mayakan na Boko Haram bangaren Abubakar Shekau sun halaka mutane uku a wani hari da suka kai a kauyen Sajeri na kusa da birnin Maiduguri, a yayin da na bangaren Al Barnawi suka kai hari a cibiyar sojoji ta garin Auno da ke nisan kilomita 23 da birnin na Maiduguri.