1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta halaka mutane 10 a Borno

Zulaiha Abubakar
February 16, 2019

A daidiai lokacin da aka dage zaben shugaban kasa a tarayyar Najeriya, mayakan Boko Haram sun kai sabon hari a yankin Arewa maso gabashin kasar da ke fama da matsalar ayyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/3DVEa
Nigeria Maiduguri Zerstörte Häuser nach Boko Haram Attacke
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Da safiyar wannan Asabar wasu ‘yan bindiga da ‘yan kunar bakin wake sun kai wasu hare-hare a unguwannin Molai da Polo da Kushari da Jadumari  a cikin Maiduguri da ke jihar Borno. Ana fargabar mutane mutane 10 sun rasa rayukansu yayin da wasu 15 suka jikata. Ko a daren jiya mayakan Boko Haram sun tare hanyar Bama zuwa Gwoza inda su ka kashe mutane 6 tare da sace mutane da dama.