1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta hallaka mutum 11 a Gomboru

Abdullahi Tanko Bala
January 3, 2018

Kungiyar Boko Haram ta ci gaba da kai hare hare inda a wannan rana ta Laraba wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane a wani masallaci a Gomboru.

https://p.dw.com/p/2qIKV
Nigeria Anschlag auf Moschee in Mubi
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wani dan kunar bakin wake ya halakka mutane goma shadaya a wani harin bam da ya kai a masallaci da safiyar laraba a yankin Gamboru na Jihar Borno a Najeriya  da ke iyaka da kasar Kamaru.

Jami'an soji da na bada agaji sun tabbatar da cewa maharin ya tada bam din ne a lokacin da ake gudanar da sallar asuba..

Kungiyar Boko haram ta saba amfani da 'yan kunar bakin wake musamman mata da kananan yara wajan kai hare-hare a wuraren taron jama'a musamman kasuwanni da wuraren ibada.