1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta kai hari Kamaru

July 27, 2014

Tsagerun Boko Haram na Najeriya sun kai hari gidan mataimakin firaministan kasar Kamaru sun kuma yi awon gaba da matarsa

https://p.dw.com/p/1CjZC
Boko-Haram-Chef Abubakar Shekau BITTE BESCHREIBUNG BEACHTEN / SCHLECHTE QUALITÄT
Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin Kamaru ya tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakaon harin da 'yan kungiyar Boko Haram na Najeriya suka kai gidan mataimakin firamnistan kasar da ke lardin Arewa mai nisa. Ministan sadarwa na kasar kuma kakakin gwamnati Issa Tchiroma ya tabbatar da labarin wa kamfanin dillancin labaran Reuters ta wayar tarho.

Wani kakakin soji na lardin ya ce 'yan Boko Haram sun yi garkuwa da matar mataimakin Firaminista Ahmadou Ali, yayin harin na wannan Lahadio a garin Kolofata da ke kusa da Najeriya. Jami'an tsaron da ke kare lafiyar mataimakin Firaministan Ahmadou Ali, sun tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya, inda suke fice da shi zuwa garin Mora.

Kasashen da ke makwabtaka da Najeriya sun amince kafa sojojin hadin gwiwa domin yakan kungiyar Boko Haram, wadda ta yi kaurin suna na hare-hare da take kai wa a Najeriya da ke shafan wasu kasashe.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba