1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta sake tada fitina a Borno

Mouhamadou Awal Balarabe
June 22, 2017

Tsaro ya sake sukurkucewa a yakin Arewa maso gabashin Najeriya musanmman a jihar Borno, Lamarin da ya sa gwamnati da al'umma nuna fargaba.

https://p.dw.com/p/2fDD4
Nigeria Boko Haram Anschlag
Hoto: picture alliance/AP Photo/J. Ola

Kungiyar Boko Haram ta umurci mazauna wasu kauyuka na jihar Borno da su kwashe nasu ya nasu su bar matsugunansu, abinda ya haifar da fargabar shirin kai hari. Dama ta yi ikirarin sace 'yan sanda mata 16, lamarin da sa gwamnatin tarayyar Najeriya nuna damuwa kan karuwar hare-haren ta'addanci.