1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zafafar hare-hare a sabuwar gwamnatin Najeriya

Al-Amin Suleiman Muhammad June 1, 2015

Tun ranar Juma’a ce dai da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki ake samun hare-hare daga mayakan kungiyar Boko Haram a jihohin Borno da Yobe abin da ya tada hankulan al’umar jihohin da kuma makobta.

https://p.dw.com/p/1Fa5N
Boko Haram Kämpfer
Mayakan Boko HaramHoto: picture alliance/AP Photo

Kungiyar Boko Haram ta zafafa hare-hare a jihohin Borno da Yobe da ke shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya lamarin ya haifar da rasa rayuka da dama tare da jikatar wasu gami da kona gidaje da ababan hawa masu yawan gaske.

A daren ranar juma'a da aka kammala rantsar sabon shugaban kasa Muhammad Buhari wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hare-haren birnin Maiduguri inda suka harba rokoki da dama cikin birnin lamarin da yayi sanadiyyar rayukan mutane 13 tare da rusa gidaje da dama.

Wani dan kunar bakin wake kuma ya hallaka mutane 26 tare da jikata wasu 28 a wannan ranar Asabar bayan da ya tashi bam da ke jikinsa a cikin wani masallaci a kusa da babbar kasuwa Maiduguri.

Nigeria Präsident Amtseinführung von Muhammadu Buhari
Sabon shugaban Najeriya Muhammad BuhariHoto: Reuters/A. Sotunde

Harin bama-bamai martani ga kalaman sabon shugaba

Haka kuma daren ranar Asabar zuwa wayewar garin Lahadi wasu ‘yan bidigar sun kai harin garuruwan Ngalda da Anzai da Fika duk a jihar Yobe inda nan ma aka kona ma'aikatu na gwamnati da gidaje gami ababan hawa na al'umma.

Wadannan hare-hare sun jefa jama'ar jihohin cikin tashin hankali kamar yadda wani mazaunin Maiduguri da bai so a bayyana sunan sa ba ya shaida wa wakilin DW ta wayar tarho.

Masana tsaro dai na kwatanta wannan sabbin hare-hare da kokarin nuna cewa har yanzu mayakan kungiyar na da sauran karfinsu duk da cewa a baya jami'an tsaron Najeriya sun yi shelar murkushe su.

Gwamnatin da ta gabata dai ta sha alwashin murkushe Kungiyar Boko Haram kafin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu sai hakan ya ci tura don kuwa ranar ake bada mulkin ma Kungiyar ta kai hare-hare a wasu sassan jihar Borno.

Angriff von Boko Haram im nordöstlichen Stadt Konduga nahe Maiduguri / Nigeria
Sojojin Najeriya da suka kwato tankar yakin Boko HaramHoto: dpa

Kyakkyawan fata ga sabuwar gwamnati

Sabuwar gwamnatin dai ta ce zata sa kafar wanda da ‘yan kungiyar domin dawo da tsaro da zaman lafi a shiyyar da ma kasa baki daya.

Al'ummar wannan yanki sun bayyana kwarin gwiwar cewa sabon shugaba kasa zai cire musu kitse a wuta dangane da matsalar tsaron kamar yadda Jamilu Muhammad ya shaida wa wakilin DW.

Yanzu haka dai ana jiran cika alkawarin da sabuwar gwamnatin ta yi na maida cibiyar bada umarni kan yaki da ta'addanaci ta rundunar sojojin Najeriya daga Abuja zuwa Maiduguri a wani bangare na kawo karshen tada kayar baya da hare-haren Kungiyar Boko Haram.