1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bolsonaro: A bani haruri kafin na karbi tallafin G7

Abdullahi Tanko Bala
August 27, 2019

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya nemi a bashi hakuri kafin ya amince ya karbi tallafin kudi daga kungiyar G7 ta kasashe masu karfin tattalin arziki domin kashe wutar daji da ta mamaye dajin Amazon.

https://p.dw.com/p/3OaG4
Brasilien Mato Grosso Waldbrände
Hoto: Amnesty International/Marizilda Cruppe

Bolsonaro yace da farko sai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nemi gafararsa sannan ya janye cin fuskar da ya yi masa yana mai cewa shugaban na Faransa ya kalubalanci 'yancin cin gashin kan Brazil game da yadda ta tunkari dubban wutar da daji da ta karade dajin na Amazon.

Kasashen G7 masu karfin tattalin arziki na duniya sun yi alkawarin baiwa Brazil gudunmawar dala miliyan 20 a yayin taron kolinsu a Faransa domin taimakawa Brazil shawo kan wutar dajin.

Macron ya baiyana halin da ake ciki a dajin na Amazon a matsayin abin da kowa ya kamata ya bada gudunmawa wanda ma yace za a iya cewa ya zama wajibi domin kare sauyin yanayi. Yace akwai bukatar kasashen duniya su dauki matakin da ya dace.

Gobarar baya bayan nan a dajin na Amazon ya samo asali ne sakamakon matakin gwamnatin Brazil na bada damar aikin hakar ma'adanai da ayyukan noma a cikin dajin inda hotunan da aka dauka na tauraron dan Adam ke yadda ake samun karuwar sare dazuka cikin gaggawa a dajin.