1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bomb ya kashe jami'in tsaro a Beirut

October 19, 2012

Ƙasashen Duniya sun yi Allah wadan harin Bomb ɗin, wanda ya haddasa asarar rayuka a birnin Lebanon

https://p.dw.com/p/16TZe
A car burns at the site of an explosion in Ashrafieh, east Beirut, October 19, 2012. At least two people were killed and 15 wounded in a roadside bomb that exploded in central Beirut on Friday, a security source said. REUTERS/Hasan Shaaban (LEBANON -Tags: - Tags: CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

Harin Bomb na mota a tsakiyar birnin Beirut ɗin ƙasar Lebanon, ya kashe wani babban jami'in tsaro da wasu mutane bakwai, tare da raunana wasu 80. Wannan hari da ya auku a lokacin cunkosan jama'a a ranar juma'a dai ya haifar da tsoro a zukatan al'ummar ƙasar, tare da danganta shi da yaƙin dake gudana a Siriya dake makwabtaka. Daga cikin mutane da suka rasa rayukansu akwai Wissam al-Hassan, dake shugabantar wani babban sashin leken asiri na Lebanon, mutumin da kuma ke adawa da gwamnatin Bashar al-Assad. Bada jimawa bane ya shugabanci wani binciken da ya gano shirin harin Bomb, wanda ya jagoranci kame ɗan siyasar lebanon dake goyon bayan gwamnatin Siriya. Tuni dai ƙasashen Duniya haɗe da fadar vatican ta paparoma da ke birnin Rome, suka yi Allah wadan harin. Fadar gwamnati Amurka ta white house ata bakin kakainta Victoria Nuland, ta danganta harin da ayyukan ta'addanci, kasancewarsa boma bomai ne da aka loda a mota.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe