1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren adawa da na goyon bayan gwamnati a Masar

July 26, 2013

Arangama tsakanin bangarorin biyu ya yi sanadiyyar rayuka tare da raunata wasu, bayan kiran da hafsan tsaro Abdel Fattah al-Sisi ya yi na a gudanar da zanga-zangar.

https://p.dw.com/p/19Erg
Proteste in Aegyten Anhänger von Mohamed Morsi und Anhänger von Armeechef Abdel-Fattah al-Sisi
Hoto: picture-alliance/dpa

Masu lura da al'amuran yau da kullum sun baiyana imanin cewar Janar al-Sisi burinsa shine ya sami goyon baya daga 'yan kasa, kafin ya dauki matakai masu tsanani kan 'yan jam'iyar yan uwa musulmi da kuma kara fadada karfin da tuni sojojin kasar suke dashi: hakan ya fito fili ganin cewar tun makafin sojojin su kayar da gwamnatin Mohammed Mursi sai da suka nemi goyon baya, kuma suka samu daga al'ummar Masar, saboda sai da dubbansu suka amsa kiran kungiyar matasa mai suna Tamarod, suka hau kan tituna kwana da kwanaki suna adawa da abin da suka kira, mulkin kama karya na Mohammed Mursi. Ko a ranar Laraba ma, sai da wannan kungiya ta baiyana goyon bayanta ga kiran da al-Sisi yayi, inda ta nemi 'yan Masar su fito su cika dukkanin wuraren taruwar jama'a a kasar, domin goyon bayan yakin da jai'an tsaro zasu fara kan aiyukan tarzoma.

Jam'iyar 'yan uwa musulmi ta nuna rashin damuwarta a game da wannan hali da aka shiga, inda ta ce ita ma magoya bayanta za su hau kan tituna ranar Jumma'a domin gudanar da zanga-zangar. Essam el-Erian ya rubuta a shafinsa na Facebook cewar wannan barazana ba zata hana dubban yan jam'iyar yan uwa musulmi su ci gaba da zanga-zanga ba. Ya kara da cewar jam'iyarsa ba zata amsa kiran da shugaban masar na wucin gadi, Adli Mansur yayi ba na shiga tattaunawar neman sulhu, saboda kamary adda yace: muna kyamar amincewa da gwamnatin dake ci a yanzu.

A member of the Muslim Brotherhood and supporter of ousted Egyptian President Mohamed Mursi holds up a mask of Mursi while gesturing during a rally around Rabaa Adawiya square, in Cairo July 26, 2013. The Egyptian army is detaining Mursi over accusations of kidnapping, killing soldiers and other charges, the state news agency said on Friday. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Saboda haka alamu dai sun nuna za'a fuskanci tashin hankali a ranar ta Jumma'a, inda kuma babu shakka za'a sanya kafa a take duk wani al'amari na are hakkin dan Adam, kamar yadda wata masaniyar al'amuran siyasa Hoda Salah tace:

Kowa sai maganar kare hakkin yan Adam da democradiya yake yi a matsayin abubuwa masu mkatukar daraja, to sai dai kowa da irin yadda ya fahimci wadannan al'amura guda biyu. A da can Mursi yayi maganar kare hakkiny an Adam, amma a zahiri yana nufin kare yan jam'iyarsa ne kawai, yayin da a yanzu suma masu maganar kare hakkin jama'a burinsu shine su take yanci da hakkin yan jam'iyar yan uwa musulmi, to amma babu mai magana.

Tun bayan da aka kawar da gwamnatin Mohammed Mursi, 'yan jam'iyarsa kusan a kullum sai sun hau kan tituna, inda duk lokacin da suka yi hakan sai an kai ga samun tashin hankali, saboda sau tari, yan kjam'iyar ta yan uwa musulmi ake fara kaiwa hari. Da farko jami'an tsaro ke da laifin haka, amma daga baya kungiyoyi dauke da makamai suka maye gurbinsu. Diana el- Tahawy masaniya a kungiyar kare hakkin 'yan Adam ta Amnesty International ta ce jami'an tsaro suna amfani da karfin da ya wuce kima , inda sau tari, babu wani dalili sukan kama duka da musgunawa yan zanga-zanga. Bugu da kari kuma, hambararren shugaba Mohammed Mursi da makusantansa ana ci gaba da tsare su tsawon makonni masu yawa a wani wurin da ba'a sani ba, ba kuma tare da an gabatar masu da sammacin laifukan da suka aikata ba. Tun da shike har yanzu ba'a tantance abin da ake tuhumar tsohon shugaban ta fuskar shari'a ba, saboda haka yan jam'iyar yan uwa musulmi suka zargi sojoi da laifin sace shi. Eltahawy ta kara dacewa:

Proteste in Aegyten Anhänger von Mohamed Morsi und Anhänger von Armeechef Abdel-Fattah al-Sisi
Hoto: picture-alliance/dpa

Ya na da muhimmanci sabbin masu mulki a Masar su nunawa duniya cewar abin da suke yi ba wani shiri ne ko daukar fansa kan yan jam'iyar yan uwa musulmi ba ko magoya bayansu. Wajibine su nuna cewar bincken da suke yi babu son zuciya a cikinsa, su kuma nuna cewar duk wadanda aka samu da aikata laifi za'a kaisu gaban shari'a, ba tare da kula da mukami ko matsayinsu na siyasa ba.

Ita ma masaniya a fannin siyasa, Hoda Salah tace burinta shine a shimfida tsarin siyasa a Masar da zai taimakawa samun zaan lafiya da kare hakkin yan jam'iyar yan uwa musulmi, wadanda wajibine a shigar dasu a duk wani mataki na sulhu da kafa sabon tushen siyasa a kasar.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani