1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin neman gurfanar da Shugaba Michel Temer

Salissou Boukari
October 17, 2018

Rundinar 'yan sandan kasar Brazil, ta nemi da mai shigar da kara na kasar da ya gurfanar da shugaban kasar Michel Temer, tare da wasu mutane 10 ciki kuwa har da 'yar shugaban kasar

https://p.dw.com/p/36f0Y
Brasilien - Temers Reaktion auf den Senat
Shugaban kasar Brazil Michel TemerHoto: Reuters/A. Machado

Ana zargin shugaban kasar ta Brazil Temer tare da wadannan mutane 10 da laifin karbar cin hanci da rashawa, da halasta kudadan haramu. Rundinar 'yan sandan ta Brazil dai ta kaddamar da wani bincike ne sama da shekara guda, domin tantance ko shugaban Temer da ke kan karagar mulkin kasar tun daga shekara ta 2016 na da hannu cikin wata badakala ta cin hanci, inda ake zarginsa da karbar toshiyar baki kafin ya amince da wani kudiri a shekara ta 2017, wanda zai taimaka wa ayyukan wasu  kamfanoni na tashoshin ruwa a kasar.

A halin yanzu dai kallo ya koma ga ma'aikatar shari'ar, ko za ta shigar da kara na shugaban kasar, ko za ta nemi a aiwatar da bincike kwakwaf, ko kuma ta yi watsi da batun. Ga kundin tsarin mulkin kasar ta Brazil dai, sai majalisar dokokin ta amince ne kotun kolin kasar za ta iya aiwatar da na ta bincike tare da gurfanar da shugaban kasar.