1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brexit: 'Yan majalisar na shirin kada kuri'a

Abdullahi Tanko Bala
January 15, 2019

A ranar Talatar nan ce 'yan majalisar dokokin Birtaniya za su kuda kuri'ar amincewa ko akasin haka akan daftarin yarjejeniyar da Firaminista Theresa May ta cimma da kungiyar tarayyar Turai EU.

https://p.dw.com/p/3BYTg
Großbritanien | Theresa May | Parlament | Brexit
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/UK Parliament/M. Duffy

Firaministar Birtaniya Theresa May na kokari a matakin karshe na jawo hankalin 'yan majalisar dokokin kasar su bada goyon baya ga shirinta na ficewar Birtaniyar daga kungiyar tarayyar Turai EU yayin da ta ke fuskantar babban kalubale na bijirewa daga wasu 'yan majalisar dokoki na jam'iyyarta da kuma jam'iyyun adawa.

A yau ne dai 'yan majalisar za kuda kuri'ar amincewa ko akasin haka akan daftarin yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar tarayyar Turai na ficewar Birtaniya daga kungiyar EU. Sai dai ana dai kyautata tsammanin za ta sha kaye a kuri'ar da 'yan majalisar za su kada.

Jama'a na baiyana ra'ayoyi mabanbanta kan yanayin da za a shiga idan 'yan majalisar basu amince da yarjejeniyar ba, da kuma ko menene zai kasance makomar Theresa May a siyasance.

A wani jawabi da ta yiwa yan majalsar dokokin a jiya Litinin May ta yi watsi da kiran da wasu ke yi na jinkirta ficewar Birtaniyar daga EU wanda aka shirya zai gudana a ranar 29 ga watan Maris.