1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

BRICS ta jinkirta kafa bankinta na raya kasa

March 27, 2013

Kasashe biyar na duniya da ke samun habakar tattalin arziki sun samu sabani tsakaninsu kan kaso da mambobin BRICS ya kamata su bayar a matsayin hannun jarin na bankin da suke niyar kafawa.

https://p.dw.com/p/185DA
Hoto: picture-alliance/dpa

Kasashen biyar na duniya da ke samun habakar tattalin arziki sun kammala taron kwanaki uku da suka gudanar a birnin Durban na Afirka ta kudu. Sanarwar bayan taro da suka fitar ta nunar da cewa sun jinkirta kafa bankin raya kasashen kungiyar BRICS wanda zai yi gogayya da manyan kafofin kudi na duniya. Ita dai Afirka ta kudu wacce ta dauki bakwancin karo na biyar na taron BRICS ta dora duk wani buri da fata kan bankin da kungiyarsu ta yi niyar kafawa. Dalili kuwa shi ne ta na so ta yi amfani da wannan damar wajen samun kudaden gudanar da ayyukanta na raya kasa musamman ma dai gine gine.

Da ma dai tun a taron da ya gudana a shekarar da ta gabata a kasar Indiya, shugaban Jacob Zuma ya nuna irin gajiyar da Afirka ta kudu za ta ci daga wannan banki. Sai dai kuma murnarsa ta koma ciki a inda maimakon kafa bankin lokacin da kasarsa ta kasance mai masaukin baki, kadamar da tattaunawa aka yi tsakanin mambobin Brics domin cimma matsaya game da alkiblar da ya kamata ya dosa. Amma dai duk da wannan jinkiri da aka samu, Zuma ya ce kungiyar kasashen da ke samun habakar tattalin arziki ta zama kadangaren bakin tulu.

BRIC BRICS Gipfel Südafrika China
Zuma bai ji dadin jinkirta kafa bankin BRICS ba.Hoto: Reuters

"Ina ganin cewa ba za a iya tattaunawa kan wani mahimmin batu ba tare da sanya kungiyar BRICS a ciki ba. A yanzu nahiyar Afirka da aka mayar saniyar ware a karnin da ya shude ta shiga cikin wani rukuni da ake ji da su."

Dalilin jinkirin kafa bankin BRICS

Babban abin da ya hana ruwa guda shi ne rashin kayyade kaso da kowace kasa za ta zuba a bakin na BRICS a matsayin hannun jari. Su dai kasashen biyar wadanda suka hada da Afirka ta kudu da Brazil da Rasha da China da kuma Indiya su na so bankin nasu ya mari hannun jari na miliyan dubu 50 na dollar Amurka: Ma'ana kowace mamba ta bayar da gudunmawar miliyan dubu 10. Rasha ce ke jan kafa a halin yanzu a inda ta nemi a rage gudunmawar zuwa miliyan dubu biyu ga kowace daga kasashen biyar.

A halin yanzu dai kasashen biyar su tsayar da watan satumba a matsayin lokacin da za su yi nazari, gabanin taron kasashe 20 da suka fi karfin tattalin arziki da zai gudana a birnin Saint-Petersburg na Rasha. Jabu Mabusa, babban jami'i a hukumar raya tattalin arzikin Afirka, ya ce Brics ba za ta iya cika burinsu da ta sa a gaba ba matikar dai ba ta tashi tsaye ba.

BRIC BRICS Gipfel Südafrika Rousseff
shugaba Rousseff ta Brazil ta kasnce kallabi cikin rawuna a taron BRICSHoto: Reuters

"Muna bukatar habaka fasaharmu cikin gaggawa, ta yadda za mu iya sarrafa damar da muke da ita i zuwa ga ci gaba gaba da kuma habakar kasuwanci."

Gajiyar da China za ta ci a kungiyar BRICS

Burin da kungiyar Brics ta sa a gaba dai shi ne shata shinge da zai bata damar rashin dogaro akan kasashen Turai da Amurka wajen samun ci gaba. Babban bankin na BRICS da suke niyar kafawa ga misali, zai ba su damar juyawa asusun bayar da lamuni wato IMF ko FMI da kuma bankin duniya baya a duk wasu al'amura da suka shafi kudi.

Sai dai kuma wasu kasashe masu tasowa na fargabar ganin cewa kungiyar ta BRICS ta zame wa china wata kafa ta samun angizo a fuskar tattalin arziki a duniya.Da ma dai sabon shugaban wannan kasa Xi Jinping ne ya zama farin wata sha kallo a taron na BRICS, kasancewa jin kadan da darewarsa kan kujerar mulkin China ya ziyarci kasashen Afirka biyu wato Tanzaniya da kuma Afirka ta kudu. Ya yi amfani da wannan dama wajen bayyanawa cewa China za ta taimaka wa kasashen Afirka da kwatankwacin miliyan dubu 15 na Euro.

BRIC BRICS Gipfel Südafrika China
Kafin Afirka ta kudu sabon shugaban China Xi Jinping ya ziyarci Tanzaniya.Hoto: Reuters

Rahotannin da suka shafi taron BRICS na kasa

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal