1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bude ofishin jakadanci a Kudus ya jawo rikici

Usman Shehu Usman
May 17, 2018

Amirka ta cika alkawarin dauke ofishin jakadancinta daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus, matakin da ya saba wa yarjejeniyar kasa da kasa, inda kuma haka ya kawo rarrabuwar kawunan kasashe n duniya

https://p.dw.com/p/2xf0f
Proteste im Gazastreifen an der Grenze zu Israel
Hoto: Reuters/I. Abu Mustafa

A ranar Litinin ce dai aka bude ofishin jakadancin na Amirka a birnin Kudus, abin da ke zuwa bayan da Shugaba Donald Trump a watan Disamba ya bayyana amincewa da birnin na Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, matakin da ya ce aniya ce ta Amirka tsawon shekaru, wanda sai a wannan lokaci mahukuntan na birnin Washington suka aiwatar.

Falasdinawa dai da ke fatan ganin gabashin na birnin Kudus ya zama babban birnin kasarsu sun yi tofin Allah tsine da matakin na Trump, yayin da sauran kasashe ke nuna fargabar cewa hakan na iya kunna rikici da Falasdinawa a yamma da kogin Jodan da yankin Gaz, a inda tuni sojan Isra'ila suka bindige Falasdinawa sama da 60 yayin da wasu sama da 2000 suka jikkata a kan iyakarsu da Gaza.