1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin Kudi na dakile yakar ta'addanci

August 10, 2020

A yayin da ake kokarin lalubo hanyar magance matsalar tsaro a Arewa maso Gabashin Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce rashin isasshen kudi ne ummul aba'isin tsawaitar rashin tsaron kasar na sama da shekaru 10.

https://p.dw.com/p/3gkqX
Nigeria Maiduguri Militär Sicherheit Anti Boko Haram 2014
Kamarin rashin tsaro a yankin Arewa maso Gabashin NajeriyaHoto: picture-alliance/epa

Tun bayan wani harin da aka kai kan gwamnan Borno makonni biyun da suka gabata dai, hakuri na masu mulki na jihohin Arewa maso Gabas da ke zaman tungar boko ta haramun, ya fara nuna alamu na kurewa.

To sai dai kuma wata ganawar da ke zaman irinta ta farko a tsakanin gwamnonin da manyan hafsoshi na tsaro da shugaban kasar a Abuja dai, ta kare da gwamnatin kasar a karon farko tana kukan babu isasshen kudi da kasar ke da bukata domin kai karshen yakin a cikin gaggawa. Wankin hula dai daga dukkan alamu ya kai gwamnatin kasar tsakar dare, bayan share shekaru har 11 ana fadin an kusa kai wa karshe amma kuma har yanzu kungiyoyin na ta'adda na cin karensu har gashinsa.
Shugaban kasar Muhammad Buhari dai ya kuma ce akwai buktar tashi a tsaye a bangare na sojojin da a cewarsa har yanzu sun gaza cimma bukatar al'ummar sassan yankin daban daban: "Rahoton gama gari da nake samu ko bayan na jami'an tsaro dai na nuna akwai bukatar kara tashi a tsaye a bangare na sojojin. Wannan gaskiya ne, labari ne da yake yawan zuwa a gareni saboda haka dole in yarda da shi. Na saurari bayanan gwamnan da yake a cikin tsakiyar rikicin, jihohin Adamawa da Bauchi da sauransu na samun zama na lafiya, ina fata zaku mutunta sadaukarwar rundunar tsaron Najeriya. Bana mamakin da akai wa gwamnan Borno shugaban wannan tafiya saboda kai ne a tsakiyar wannan rikici. Ina baka tabbacin cewar gwamnati na iyakar kokarinta, amma rashin isasshen kudi na dukanmu kwarai da gaske. Ina baku tabbaci gwamnonin arewa  maso gabas musamman ma gwamnan Borno, cewar muna kwana da tashi da tunanin matsalolinku da kuma yadda zamu samar da tsaro a kasarmu saboda babban alhaki na gwamnati shi ne batun tsaro."

Afrika Nigeria Borno Professor Babagana Umara Zulum
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara ZulumHoto: Government House, Maiduguri, Borno State
Nigeria Präsident Mohammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

To sai dai koma ya zuwa ina mafarkin na gwamnatin ke iya kai wa a kokari na neman mafitar annobar ta  ta'adda, gwmnonin dai sun ce suna da bukatar neman mai da daukacin al'ummar yankin ya zuwa sano'in gado irin nasu noma da batun kiwo, abun kuma da a cewar shugaban kugiyar gwamnonin yankin kuma gwamnan Borno  Babagana Umara Zulum ke zaman guda tsakanin yankin da tabbatar da dorarren zama na lafiya a cikinsa. Kuma kama daga zargin sojan kasar da yin zagon kasa ya zuwa neman karin karfi ga rundunar 'yan sanda da nufin tunkarar rikicin dai, gwamnonin sun nuna alamun dawowa daga rakiyar tsarin da gwamnatin kasar ke bi, wanda ya damka daukaci na alhakin yakin na ta'adda a hannun sojoji.

Batun na kamun  kifi a  garuruwan da ke bakin tafkin na Chadi dai, na zaman babbar sana'a ta dogaro a bangare na sojojin Tarayyar Najeriyar da ke mata kallon hanyar arzikin dare daya, da su kansu 'ya'ya na kungiyoyin na ta'addan da ke karba ta harajin kifin,