1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya gana da shugabannin majalisu

Abdul-raheem Hassan
March 16, 2018

Shugabannin majalisun dattawa da na wakilai a Najeriya sun tattauna matsalolin da ke tsakanin su da shugaban kasa wannan dai wani mataki ne dinke baraka tsakanin bangaren zartarwa da na majalisun.

https://p.dw.com/p/2uSbd
Nigeria Präsident Muhamadu Buhari
Hoto: Novo Isioro

Taron ya dauki lokaci ana sa in sa, sai dai an cimma matakai tsakanin shugaban kasa da ya sa kafa ya shure muradun  'yan majalisun. Rikicin ya faro ne bayan bukatar majalisar dattawa na maye gurbin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta EFCC Ibrahim Magu bukatar kuma da shugaban kasar ya ce ba hali.

Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Buhammadu BuhariHoto: DW/I. U. Jaalo

Ko bayan nan dai Buhari ya yi watsi da dokokin rundunar zaman lafiya ta Peace Corps da dokar zabe ta shekara ta 2018 da majalisun kasar suka amince. Wannan ya sa 'yan majalisun suka tsaida aikin tantance jami'ai na gwamnatin dama manta da batun kasafin kudin kasar.

Nigeria Bukola Saraki
Shugaban majalisan dattawa, Bukola SarakiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Duk da  cewar an kai ga gudanar da taron a cikin sirri daga dukkan alamu an kai ga fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Senator Bukola saraki ya ce "Taron yayi tasiri, saboda munsamu damar ba da tamu guddumuwa a kan batutuwanda taron ya maida hankali."

Gwamnatin kasar ta umarci ma'aikatu da hukumomin gwamnati da su koma majalisun kasar domin ci gaba da aikin kasafin kudi.