1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya kaddamar da rundunar yaki da satar shanu

Mouhamadou Awal BalarabeJuly 13, 2016

Barayin shanu da 'yan fashi na jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya za su gamu da fishin soji daga yanzu idan suka sake aikata ta'asa, lamarin da ke zama kalubale ga rundunar kasar da ke yakar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1JOSf
Nigeria Muhammadu Buhari Präsident Rede vor der UN Vollversammlung
Hoto: Getty Images/AFP/M. Ngan

Buhari ya kaddamar da rundunar yaki da satar shanu

Sace-sacen shanu a yankin Arewa maso yammacin Najeriya sun kai ga kashe Fulani makiyaya a shekarun baya-bayannan. Saboda haka ne a shekara ta 2015 gwamnonin wannan yanki suka kafa rundunar hadin gwiwa ta jami'an tsaro, wadda aka dora wa nauyin shiga dajin da barayin shanu ke aikata munanan ayyuka don ja musu birki.

Sai dai al'ummar Arewa maso Yammacin Najeriya sun ta korafi kan wannan runduna, inda suka ce ba shi da tasirin a zo a gani saboda ana ci gaba da zubar da jini. Saboda haka ne gwamnatin tarayya ta shiga cikin harkar, inda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da rundunar sojoji ta musamman domin yaki da barayin shanun.

Nigeria Soldaten in Damboa
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Ministan Tsaro Mansur Dan Ali, ya ce akalla dakarun sojojii dubu ne za a tura a yanzu haka. Sai dai za a kara adadinsu daga bisani. Wannan lamari dai ya zo ne a daidai lokacin da jami'an tsaron Najeriya ke yaki da Boko Haram, lamarin da ke zame musu wani sabon kalubale.