1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi hadin kan ECOWAS don tabbatar da tsaro

Abdoulaye Mamane Amadou
June 29, 2019

Shugabannin da gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka Ecowas sun soma wani zaman taron koli karo na 55 a yau Asabar a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya

https://p.dw.com/p/3LKnL
Nigeria Abuja ECOWAS Konferenz
Hoto: DW/Katrin Gänsler

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen da su tashi haikan don tunkarar matsalolin tsaro musamman ma na 'ataddanci da fadace-fadacen kabilanci da ke addabar yankin na yammacin Afirka.

A cewar Buhari, baya ga matsalolin batun rigingimu da ke tasowa tsakanin makiyaya da manoma na zaman wata babbar barazanar da ke kara kawo rarrabuwar kawuna da rashin hadin kai tsakanin al'ummomin yankin, kana kuma rikice-rikicen na zama karfen kafa ga bunkasar tattalin arzikin al'umma da kuma zama karfen kafa ga ayyukan da hukumomi ke yi don kyautata rayuwar jama'a.

Taron na zuwa daidai lokacin da batun tabarbarewar tsaro ke kara addabar yankin musamman ma na ta'addanci da ya mamaye kasashen Najeriya Nijar Mali da Burkina Faso.

Ko baya ga batutuwan tsaro taron na wuni daya zai kuma duba batun kudaden bai daya d yankin na yammacin Afirka ke son soma amfani da su a shekarar 2020.