1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya rantsar da sabbin jami'an gwamnati da ya nada

Ubale Musa Dw Abuja/ MNAAugust 31, 2015

Duk da koke-koken 'yan adawa game da sabbin nade-naden mukamai a gwamnatin Najeriya, shugaban kasar ya rantsar da sabbin jami'ansa.

https://p.dw.com/p/1GOhp
Muhammadu Buhari Präsident Nigeria Porträt G7 Gipfel 2015 Schloss Elmau
Hoto: picture-alliance/dpa/Minkoff

A wani abin da ke zaman uwar watsi da adawa da koke-koken da suka mamaye nade-nade mafi tasiri a cikin gwamnatin da ke da watanni uku, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sakataren gwamnatin kasar da kuma mashawartan tsaro da kakakin fadarsa.

An dai dauki sama tare da kokari na jawo ta a kan kasa bayan da babu zato ba kuma tsammani shugaban kasar Muhammad Buhari ya bada sanarwar nadin manyan mukamai biyu na babban hafsan mulkin fadar gwamnatin kasar da sakataren da zai ja ragama ta gwamnatin daga yanki guda daya.

Manyan mukamai daga shiyya guda

Nadin na Babachir David Lawal daga jihar Adamawa sannan kuma da Alhaji Abba Kyari daga Borno domin rike mukaman biyu mafiya tasiri dai ya hadu da korafi daga masu tunanin sai kansu, da kuma suka ce shugaban ya saba ka'idar da ke akwai a halin yanzu.

Niger Buhari Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

To sai dai kuma daga dukkan alamu Buharin yayi kunne na uwar shegu da korafin tare da rantsar da sabon sakataren gwamnatin kasar Babachir David Lawal da kuma mashawarta na tsaro da kakakin fada.

A wani bikin da ya samu halartar manyan jami'ai na gwamnatin da hafsoshi na tsaro dai shugaba Buharin ya kauce wa al'ada wajen rantsar da jami'an ba tare da cewa uffan ko dai a bisa jerin zargin zabe a wuri guda ko kuma umarni da ke zaman al'ada a biki irin na rantsuwa.

Ana dai kallon nade-naden biyu a matsayin kokari na dorawa a bisa salo na ba zatar da yayi nisa a ciki da kuma ya sanya karatun alkiblar da gwamnatinsa ke shirin dauka a gaba.

Kusan biyu a cikin uku na jami'ai da suka yi nasarar gano sunayensu a jerin nadi kusan 40 da ya fito fili ya zuwa yanzu, ko dai ba a sansu cikin harkoki na siyasa ba, ko kuma suna can kasa cikin jerin mutanen da ake da tunanin Buharin zai dauka domin taimaka masa sauke alkawuran yin canjin.

To sai dai kuma ana kallon jan aiki a wuyan su kansu masu ci a halin yanzun da ke zaman limamin canjin da kuma 'yan kasar da ma bakinta ke yi wa tsammanin jan ragamar kasar zuwa tudun mun tsira.

To sai dai kuma a fadar sabon sakataren na gwamnatin aikin sauya kasar na tsakar kan kowa maimakon yaya na kalilan din da suka yi rantsuwa ta kamun aikin yanzu.

Korafe-korafe daga bangarori daban-daban

Tabbatar da adalci kan kowa da nufin gyaran lamura na kasa, dai tun ba a kai ga ko'ina ba kungiyoyi na kabilu daga sassan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudanci na kasar suka fara karatun ba adalci a cikin sabon sauyin na Buhari.

Nigeria Regierungspartei PDP
PDP na daga cikin masu daga murya wajen sukar nadin da Buharin yayiHoto: DW/K. Gänsler

Ita ma dai jam'iyyar PDP ta adawa ta ce da sauran sake ga salon tafiyarwa ta Buharin da ma yadda jami'ai na gwamnatinsa ke bulla ya zuwa yanzu.

To sai dai kuma a tunanin Lawalli Shua'ibu da ke zaman mataimakin shugaban Jam'iyyar APC ta Buharin duk wani korafi kan sabo na nadin bai wuci rashin hakuri da me ka shuka a cikin tsarin da ke da niyyar yin 'ya'ya a kankane na lokaci.

Akalla mukamai guda 6,000 ne dai ake sa ran shugaban zai kai ga nadawa a cikin tsawon mulkin nasa na shekaru hudun da ke tafe.