1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren MDD ya nemi a ceto kasashe daga yunwa

February 23, 2017

Majalisar Dinkin Duniya na bukatar miliyoyin daloli don maganta matsalar abinci cikin kasashe hudu.

https://p.dw.com/p/2Y6vL
Guterres UN PK zu Hungersnöte in Afrika
Babban Sakataren Majalisar Dinkin DuniyaHoto: picture-alliance/Zumapress/A. Lohr-Jones

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteres, ya yi kiran gaggawa na hadin kan kasashen duniya don samun akalla dala biliyan hudu da rabi da a yi amfani da su wajen ceto kasashen da ke fuskantar hadarin yunwa a bana. Kasashen da matsalar za ta shafa dai su ne kasar Sudan ta Kudu da Najeriya da Somalia da kuma kasar Yemen. Sakataren na Majalisar Dinkin Duniyar Mr. Guteres ya ce dala miliyan 90 ne ke a hannu ya zuwa yanzu, lamarin da kuma ke bukatar tallafi cikin hanzari.

Hasashe ya yi nunin cewa sama da mutane miliyan 20 ne za su fuskanci matsalar abinci a watanni 6 nan gaba, lamarin ma da tuni aka soma ganinsa a kasar Sudan ta Kudu. Kalaman Mr. Guteres dai sun yi nunin cewa wasu jami'an MDD da kungiyoyin agaji ma sun riga sun nuna manyan alamun faruwar wannan matsala a kasashen 4.