1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar zaman lafiya tsakanin Manyan addinai

October 11, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8f

Malaman addinin Islama sama da 130 daga sassa daban daban na duniya ne ,sukayi kira dangane da bukatar fahintar juna tsakanin musulmi da mabiya addinin krista.A wasikar da aka aikewa Paparoma Benedict na 16,da sauran manyan shugabannin Christa,Malaman sun jaddada cewar zaman lafiya tsakanin manyan addinan biyu,shine zaman lafiyan duniya baki daya.Wani Sheihin malami dake Jamia’ar Cambridge a Britania,Aref Ali Nayed,yace wasikar na wakiltan kashi 99.9 na alummar musulmi.Dangantaka tsakanin Musulmi da christoci dai,ya fuskanci matsaloli ,tun bayan harin 11 ga watan satunban 2001 akan Amurka da yake yaken Afganistan da Iraki.