1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bremen feier

October 3, 2010

A wannan Lahadin shagulgulan da aka fara tun wancan mako domin bukin cika shekaru 20 na samun haɗin kan gabashi da yammacin Jamus ke kai ƙololuwarsu.

https://p.dw.com/p/PTMv
Dubban mutane suka hallara a birnin Bremen inda aka gudanar da bukin cika shekaru 20 da sake haɗewar JamusHoto: picture-alliance/dpa

An fara shagulgulan na wannan rana ne da wani zaman coci da aka yi a birnin Bremen, da a wannan karo ke jagorantar bukin. Shugaban ƙasar Jamus, Christian Wulff ya gode wa ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙasashen da suka ba da tasu gudunmuwa wajen samar da haɗin kan Jamus. Ya miƙa godiyarsa musamman ga al'umar gabashin Jamus waɗanda ya ce sune suka yi gwagwarmayar samar da 'yanci suka kuma ɗauki nauyin sauye-sauyen da aka fuskanta a dangane da sake haɗewar ɓangarorin biyu. Wulff ya kuma bayyana ƙalubalen dake a gaban haɗaɗɗiyar ƙasar ta Jamus, yana mayar da hankali ga matsalar da ake fuskanta game da sajewar musulmi dake zaune a Jamus-abin da ya haifar da zazzafar muhawara a baya bayan nan.

Yace:"Ko da yake addinnan Krista da Yahudanci na da dadaɗɗen tarihi a Jamus a yanzu addinin Musulunci shi kuma ya zama wani ɓangare na ƙasar."

Yayi kira ga ɗaukacin waɗanda ke zaune a Jamus da su rinƙa biye wa dokokin tsarin mulki ƙasar da kuma salon rayuwarta, kana su kuma mayar da hankali ga koyon harshen Jamusanci.

A ɗayan hannun kuma shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel wadda ta girma a gabashin Jamus, tunawa ta yi da rayuwar da ta yi a ƙarshin tsarin kwaminisanci. Merkel wadda ake wa kallon ɗaya daga cikin mata masu kamar maza a duniya tace ko da wasu matsaloli da aka fuskanta a Jamus ta Gabas an samu jin daɗin rayuwa.

Shugaban Amirka Barack Obama ya taya Jamus murna a dangane da wannan rana tare da jinjina wa al'umar Jamus bisa ƙarfin zuciyarsu da ya kai ga wargaza kantagar Berlin da kuma yayi sanadiyar sake haɗewar ɓangarorin biyu.

Shugaba Dmitry Medvedev na Rasha shi kuma ya taya Jamus murna inda yace sake haɗewar gabashi da yammacin Jamus wani muhimmin abu ne na tarihi ba ma ga Jamus kaɗai ba, amma har da baki ɗayan nahiyar Turai.

Wannan buki ya kuma yi kicibis da ranar da Jamus ta biya ragowar kuɗin diyya da aka bita tun bayan yaƙin duniya na biyu, wanda wata yarjejeniya da aka sanya hannu akanta a birnin Versailles na ƙasar Faransa a shekarar 1918 ta tanadi bayar da shi. Bayan haka ne kuma aka rattaba hannu akan wata yarjejeniya ta daban a shekarar 1953 wadda ta buƙaci Jamus da ta biya ƙarin ruwa akan kuɗin na diyya in har ta nemi ta sake haɗewa. A ranar 3 ga watan Oktoban 1990 Jamus ta biya ragowar Deutsche Mark miliyan 240 na kuɗin diyyar. A yanzu Jamus ta kammala biyan wannan kuɗi bayan shekaru 20, kuma shekaru 92 tun bayan yaƙin duniya na farko. A shekarar 1988 ne dai Jamus ta biya kuɗin diyya game da yaƙin duniya na biyu.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Mohammad Nasiru Awal