Bukin zagoyowar ranar kisan kiyashi a Srebrenica
July 12, 2013A dangane da hakan ne an sake yin biso ga gawawwakin 409 da aka gano,duk kuwa da ruwan sama da ake tafkawa kamar da bakin kwarya. Daga cikin wadanda ake sake yi wa bison har da wata 'yar jaririya da sojojin sa-kai na Serbiya suka halaka, jim kadan bayan da aka haifeta. Ga baki daya dai gawawwaki sama da dubu shida aka sake yi wa biso a daura da bukin zagoyowar wannan rana. Shi dai kisan kiyashin da ya faru a Srebrenica na zaman irinsa mafi muni da aka fusknta a nahiyar Turai tun bayan yakin duniya na biyu- abin da kotun hukuntan lefukan yaki da aka kafa akan tsohuwar kasar Yugoslavioya da ke a birnin Hague na kasar Holland ta kira kisan kare dangi.
A dai halin yanzu ana ci gaba da tuhumar Radovan Karadzic, wanda shine ya ba da umarnin aikata wannan ta'asa. Ita dai kotun da ke a birnin Hague ta kara daga laifukan da ake zargin Karadzic da aikatawa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu