1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bullar 'yan takarar shugabancin kasa a Nijar

Salissou KakaDecember 28, 2015

Jam’iyyun siyasa na ci gaba da bayyana sunayen 'yan takararsu da suka tsaida a zaben shugaban kasar mai zuwa na 21 ga watan Febireru na 2016.

https://p.dw.com/p/1HUkC
Mahamane OusmaneHoto: picture-alliance/dpa

Bayan takarar Kassoum Mahaman Moktar a karkashin tutar jam'iyyar CPR Inganci, da takarar Sheffou Amadou karkashin tutar RSD Gaskiya, jamiyyar MPN Kishin kasa ta tsaida kanal Ibrahim Yakouba shugaban jamiyyar a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa da za'ayi a watan Febireru na 2016 mai shirin kamawa, inda ya nuna farincikin shi sosai da wannan nauyi da magoya bayansa suka dora masa.

Abdou Labo
Abdou LaboHoto: DW/M. Kanta

Shi ma Kassoum Mahaman Moktar da jamiyarshi ta CPR Inganci ta tsaidashi a watan Nuwamba da ya gabata a birnin Zinder na zaman daya daga cikin 'yan takarar da ke alfari da jihar Maradi inda ya jaddada wannan aniya ta shi tare da fatan taka rawar gani a cikin wannan jiha. Sai dai yayin da wasu shugabannin jamiyoyin siyasa suka bayyana matsayin jamiyyarsu na goyon bayan bangaren gwamnati ko adawa, jamiyyar ta MPN kishin Kasa ta tabakin dan takararta Ibrahim Yakouba ba za su goyu bayan kowaba har sai sun gwada karfinsu a fadadin kasar ta Jamhuriyar Nijar. Bayan ma wadannan 'yan takara biyu da suke bugon gaba da wannan birni na Maradi, akwai kuma Cheffou Amadu, wanda shi ma jam'iyyarsa ta RSD Gaskiya ta tsayar da shi wanda kuma sanin kowa ne Maradi ita ce cibiyar wannan jam'iyya kuma nan ne ta fi samun babban kaso a fagen zabe.

Kowace jam'iyya na son nuna karfinta

Hakan dai na zuwa ne kuma a daidai lokacin da wata jam'iyya da ake kira MNRD Hakuri ita kuma ta tsayar da tsofon shugaban kasa Alhaji Mahamane Ousmane a matsayin dan takararta duk kuwa da cewa ba dan jam'iyyar ba ne abun da masu lura da al'ammura ke ganin cewa hakan na a matsayin daukan wani mataki kan rikicin da suke na samun shugabancin jam'iyyarsu ta CDS Rahama tare dada Abdou Labo da shi ma ke bugon gaba da jihar ta Maradi wanda tuni shi ma ya tsaya takara a karkashin inuwar jam'iyyar ta CDS Rahama duk kuwa da cewa rikicin na su na a gaban kotu. Da farko dai Jam'iyyar Moden FA Lumana ce ta tsayar da Hama Amadou, yayin da jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya ta sake tsayar da Shugaba Issoufou Mahamadou, inda babbar jam'iyyar adawa ta MNSD Nasara ta tsayar da Shugabanta Alhaji Seini Oumarou.

Seini Oumarou
Seini OumarouHoto: MNSD