1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bunkasar matsugunan Isra'ila a yankunan Palesdinawa

January 2, 2013

Kunci da tsadar rayuwa suna kara ingiza 'yan Isra'ila ga samun sabbin wuraren zama a matsugunan Yahudawa a yankunan da kasar ta mamaye.

https://p.dw.com/p/17CWp
Hoto: picture-alliance/Hanann Isachar

Mazauna kasar Isra'ila suna kara shiga cikin wani hali na matsi, sakamakon tsanantar tsadar rayuwa. Iyalai masu yawa a kasar, musamman matasa suna ganin hanya daya kawai ta rage masu da zasu kaucewa wannan yanayi. Wannan hanya kuwa ita ce suyi kaura zuwa sabbin matsugunai da gwamnatinsu ta kafa a yankunan Larabawa da ta mamaye. Gwamnatin ma ta kan yi amfani da kudi domin jan hankalin iyalai zuwa wadannan matsugunai.

A bayan da Palesdinawa a karshen watan Satumba suka sami yancin kujerar zama yar kallo a zauren majalisar dinkin duniya a New York, Israila cikin gaggawa ta sanar da cewar zata hamzarta matakinta na giggina matsunan Yahudawa a yankunan Palesdinawan da ta mamaye a gabashin birnin Kudus da yammacin kogin Jordan. Tace zata gina karin gidaje 2600 a Givat Hamatos da 1200 a Gilo da kuma gidaje 1500 a garin Ramat Schlomo, duk kuwa da sanin cewar wadannan matsugunai tun asalinsu ma, sun sabawa dokokin duniya, saboda haka na haramun ne.

Kamar yadda Israilan tace, shirin fadada wadannan matsugunai tuni aka gabatar dashi, kuma wai babu wata dangantaka tsakanin sanar da gine-ginen a bainar jama'a da lokacin da Palesdinawa suka sami kujerar yan kallo a majalisar dinkin duniya. A yan kwanakin hutun Kirsimeti kuma, ministan tsaro, Ehud Barak ya sanar da cewar an daga matsayin babbar makarantar dake wani matsuguni mai suna Ariel zuwa ga matsayin jami'a. Tun da kuwa yankin na yammacin kogin Jordan da gabashin birnin Kudus suna karkashin mamaye ne, saboda haka sojoji ne suke da alhakin kula da al'amuran samar da ilimi a wadannan yankuna. Sarit Michaeli, kakakin kungiyar kare hakkin yan Adam mai suna B'tselem tayi nuni da cewa:

Gaza Konflikt Waffenruhe Benjamin Netanyahu
Pirayim Ministan Israila Benjamin NetanyahuHoto: GALI TIBBON/AFP/Getty Images

"Wannan ba komai bane illa wani karin mataki na Israila na canza tsarin layin da ya raba iyakokin Palesdinawa da yankunan da ta mamaye. Kokari suke yi su ja hankalin yan Israila cewar wai babu wani banbanci ko mutum yana zaune a cikin ita kanta Israila ne ko kuma a yankunan da ta mamaye."

Israilan tun daga yan shekarun baya ta kashe kudi mai yawan gaske a fannin fadada matsugunan nata. An kashe kudi wajen jan hankalin mutane zuwa garesu, yadda yan kasar da dama suka karbi wannan tayi, musamman saboda kaucewa kara tsanantar tsadar rayuwa a kasar. Mazauna wadannan matsugunai na Yahudawa ba gaba dayansu ne masu matsanancin ra'ayin addinin Yahudanci ba, dake zuwa can domin tabgbatar da mafarkinsu na samun katuzwar Israila tun daga kogin Baharrum har zuwa gabatar kogin Jordan.

Gilli Paran dan shekaru 29, dake zaune a Ramat Gan, wani yanki dake bayan garin Tel Aviv, a kullum yakan yi tafiya zuwa jami'ar dake Samaria, kamar yadda ake kiran babbar makarantar da aka daukakata a garin Ariel. Yace wadannan matsugunai na Israila suna da matukar muhimmanci.

Israel Ariel Universität
Jami'ar Samaria a matsugunin Ariel dake yammacin kogin JordanHoto: picture-alliance/Hanann Isachar

"Daukar karatu a jami'ar abu ne mai kyau, saboda azuzuwan babu dalibai masu yawa dake cunkushe su, ga kuma isassun kayan aiki. Ana zuba kudi mai yawa a jami'ar ta Ariel."

Suma matasa musamman ana jan hankalin su ta hanyar kyautata matakan jin dadin zamansu a matsugunan, idan aka kwatanta da tsadar rayuwa da karancin gidaje da tsadar kudin haya misali a birnin Tel Aviv. Masharhanta suka ce Israila da gangar take fadada matsugunan nata a yankunan Larabawa da ta mamaye, yadda zuwa gaba, zai zama abui mai wahala a tilasta mata tayi wnai sassauci idan aka nemi ta janye daga wuraren da ta mamaye a yanzu.

Mawallafa: Florian Mebes / Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal