1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da fitilu masu aiki da zafin rana a Burkina faso

Salissou Boukari
October 16, 2016

A karon Burkina Faso ta kaddamar da kamfanin kera fitilu masu aiki da zafin rana, wanda kai tsaye ake ganin za su canji fitillu masu amfani da kalanzir a kasar da ke da karancin wutar lantarki.

https://p.dw.com/p/2RH2t
Afrika Kenia Solar Lampe
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Tun dai daga ranar Alhamis da ta gabata ne kamfanin ya soma buda kofofinsa a birnin Dedougou da ke a nisan kilomita 265 a yammacin Ouagadougou babban birnin kasar. Wanda ya kirkiro wannan kamfani wani Bafaranshe mai suna Arnaud Chabanne ya sanar a yayin kaddamar da kamfanin cewa, kokarinsu shi ne na ganin sun samar wa miliyoyin al'ummar kasar ta Burkina Faso wannan fitila mai aiki da zafin rana.

Kasar ta Burkina Faso dai da ke a matsayin daya daga cikin wadanda suka fi fama da talauci a duniya, na fuskantar matsalar tsadar wutar lantarki, inda kashi 19 cikin 100 na al'ummar kasar da yawanta ya kai miliyan 19 ne ke samun wutar lantarki a kasar.

Hukumomin kasar dai sun sha alwashin magance wannan matsala ta wutar lantarki, inda a watan Yuni da ya gabata suka kaddamar da ayyukan gina cibiyar samar da wutar lantarki mai aiki da zafin rana da ke a matsayin mafi girma a yankin Sahel.