1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso ta samu sabon shugaba

Yusuf BalaNovember 17, 2014

Bayan kwashe tsawon lokaci ana tafka muhawara, masu ruwa da tsaki na kasar Burkina Faso sun amincewa Michel Kafando ya jagoranci gwamnatin rikon kwaryar kasar.

https://p.dw.com/p/1Dogp
Michel Kafando Übergangspräsident Burkina Faso 17.11.2014
Hoto: AFP/Getty Images/Stringer

Ga alama dai a iya cewa rikicin siyasar Burkina Faso ya fara zuwa karshe domin kuwa 'yan siyasa da malaman addini da kungiyoyin fararen hula da suka kwashe tsawon lokaci suna tattaunawa da ma tabka mahawara sun amince da fitar da Michel Kafando a matsayin mutumin da zai jagoranci kasar a mataki na rikon kwarya.

Bayan amincewa da nadin nasa dai, Mr. Kafando dan shekaru 72 da haihuwa ne kana masanin harkokin diflomasiya ya bayyana cewa a shirye ya ke da ya bada gudunmawarsa wajen ciyar da kasar gaba saboda girmamawar da aka yi masa, inda ya kara da cewar ''babban nauyi ne aka aza mani na jagorantar wannan rikon kwaryar, kuma tun yanzu na tabbatar da cewa ba karamin aiki ba ne a gabana.''

Proteste nach Militärputsch in Bukina Faso 02.11.2014
Boren al'umma na nuna kosawa da mulkin Blaise Compaore ce ta kawo sauyi a kasarHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Bayyana sunan Mr. Kafando a matsayin shugaban Burkina Faso na rikon kwarya dai ya zo wa wasu da mamaki domin kuwa ba a yi zaton zai kai ga samun wannan kujera ba, hasalima an fi ganinta ko dai a hannun babban limamin addinin Kirista na Bobo-Diou-Lasso wato Paul Ouedraogo ko kuma Sherif Cy wanda ya mallaki wata jarida da ta shara wajen wajen sukar gwamnatin tsohon shugaba Blaise Compaore, ko kuma wani dan jarida Newton Ahmed Barry da dai sauransu.

Tuni dai wasu daga cikin wanda ake yi zaton za su samu wannan mukami suka yi mubayi'a ga sabon shugaban inda guda daga cikinsu wato Sherif Cy ya ce "ina taya shi (Michel Kafando) murnar samun wannan mulki da aka ba shi sai dai matsayi ne mai nauyi kana da jan aiki a gabansa kasancewar akwai matsaloli na siyasa da wannan kasa (Burkina Faso) ke fuskanta."

Blaise Compaore Präsident Burkina Faso
Shugaba Compaore dai ya shafe shekaru 27 kan mulki kafin a kawar da shiHoto: REUTERS

Nan gaba ne dai ake sa ran Kafando zai bayyana sunan firaminista da zai kafa gwamnati mai mambobi 25 to sai dai ba zai shiga a dama da shi ba cikin fafutukar neman darewa mulkin wannan kasa ta Burkina ba a zaben da za a yi a karshen shekara mai kamawa.