1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina: Harin ta'addanci a birnin Ouagadougou

Ramatu Garba Baba
August 14, 2017

Wasu da ake zargin mayakan jihadi ne sun kashe mutane akalla 18 a wani hari da suka kai a gidan cin abinci na Turkawa da ke Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/2iBqR
Burkina Faso Tag nach dem Angriff in der Kwame Nkrumah Avenue in Ouagadougou
Masu ayyukan ceto bayan harin da aka kai a gidan cin abinci da ke OuagadougouHoto: Reuters/B. Pare

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar ta Burkina Faso ta tabbatar da mutuwar mutane 18 da suka hada da 'yan kasar ta Burkina da kuma wasu 'yan asalin kasashen ketare ba tare da bayyana takamaiman kasashen ba. Sai dai gwamnatin Faransa ta bayyana cewa akwai akalla Bafaranshe daya daga cikin mutanen da suka mutu a harin. Wani abin da har ya zuwa yanzu mahukuntan na Burkina ba su kai ga tantancewa ba shi ne adadin mutanen da suka kai harin da ma wanda ya ke da alhakin kai harin. A yayin da wasu shaidu ke bayyana cewa mutane biyu ne a saman babur dauke da bindigogi kirar Kalachnikov, wasu kuma na cewa maharan sun zo ne a cikin mota kirar Toyota. Sai dai kuma mahukuntan sun sanar da harbe biyu daga cikin maharan da misalin karfe biyar na asubahi bayan da aka share awoyi ana musayar wuta da su. 

Harin ya haifar da daurin kai

Wani batun na dabam da ke ci gaba da haifar da muhawara biyo bayan wannan harin da aka kai a gidan cin abinci da ake kira "Cafe Restaurant Aziz Istanbul" da ke birnin na Ouagadougou, shi ne na dalilin da ya sanya a ka kai shi.

Burkina Faso Tag nach dem Angriff in der Kwame Nkrumah Avenue in Ouagadougou
Gidan cin abinci na Cafe Restaurant Aziz Istanbul da ke OuagadougouHoto: Reuters/B. Pare

A yayin da wasu ke cewa harin ta'addanci ne na masu kishin iIslama, wasu kuma na dora alhakin hari ga tsohuwar Gwamnatin Blaise Compaore wacce yanzu haka ake ci gaba da tsare wasu daga cikin shika-shikanta a gidajen kurkukun kasar.

Faransa da Burkina sun jaddada aiki tare da juna

Bayan afkuwar wannan lamari dai Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tattauna a wannan Litinin din ta wayar tarho da takwaransa na Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, inda suka jaddada bukatar ci gaba da karfafa hulda tsakanin kasashensu wajen yaki da ta'addanci, da ma gaggauta girka rundunar yaki da ayyukan ta'addanci a yankin Sahel ta G5 Sahel, kana sun sha alwashin sake tuntubar juna a kwanaki masu zuwa.