1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cameron ba zai shiga yakin Syriya ba

August 30, 2013

Majalisar dokokin Birtaniya ta yi fatali da take-taken firaministan David Cameron na shiga sahun wadanda za su afka wa syriya da yaki sakamakon zargin amfani da makami mai guba.

https://p.dw.com/p/19Yq7
Hoto: Reuters

Firaministan Birtaniya David Cameron ya gaza samun goyon bayan majalisa da ya bukata wajen shiga cikin rukunin kasashen da ke da niyar afka wa Syriya da yaki sakamakon zargin al-Assad da ake yi da amfani da makami mai guba a kan fararen hula. Tuni ma dai Cameron ya bayyana aniyarsa ta mutunta kudirin da 'yan majalisan Birtaniya suka albarkanta.

"A fili ya ke cewa majalisa ta yi watsi da kudirin da aka shigar gabanta. Majalisa da ke wakiltan 'yan Birtaniya ta fito balo balo ta nuna adawarta ta afka wa Syriya da yaki. Na ji wannan sako, sannan zan yi aiki da shi."

'Yan majalisan Birtaniya 285 ciki har da 'yan jam'iyyar Cameron ne suka yi watsi da duk wani yunkuri na yaki a Syriya yayin da 272 suka yi na'am da shi. Wannan ya na nufin cewa Birtaniya ba za ta jera da Amirka ba idan Barack Obama ya yanke shawarar daukan matakin soje a kan gwamnatin al-Assad.

Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma shugaban Rasha Vladimir Putin sun yi kira da a jira sakamakon binciken da Majalisar Dinkin Duniya ke gudanarwa yanzu haka a Syriyan kafin daukan wani mataki a wannan kasa. Wata kididdigar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar ta nunar da cewa kashi biyu bisa uku na Jamusawa na adawa da duk wani mataki na soje a kasar Syriya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu