1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Canji sheƙa na 'yan siyasar Nijar

January 14, 2014

Ɗaya daga cikin jiga-jigai na jam'iyyar Modem Lumana Afrika Alhaji Zaku Jibbo Zakai wani na hannun daman Hama Amadu ya koma jam'iyyar da ke yin mulki PNDS Tarraya.

https://p.dw.com/p/1AqTL
Hama Amadou bei der ersten Wahlrunde im Niger
Hoto: picture-alliance/Photoshot

A ƙarshen makon da ya gabata ne dai Alhaji Zaku Jibbo wanda ake yi wa laƙabi da sunan Zakai baban ƙusa a jam'iyyar shugaban majalisar dokoki Hama Amadu wato Modem Lumana Afrika ya shirya wani ƙasaitaccen biki a garinsu na Wallam mahaifarsa, inda a can ya bayyana sheƙar zuwa jam'iyyar ta PNDS Tarrayar mai mulki. Da ya ke mayar da martani kakakin jam'iyyar Alhaji Lawali Salisu.Ya ce '' Daman mun sa haka za ta faru saboda matsin lambar da jam'iyyar da ke yin mulki ta ke yi ga 'yan siyasa abin da ke tsorata su.''

Ana shirin gurfanar da Zakan a gaba kotu a kan zargin cin hanci.

Wanann canjin sheƙar siyasar ya zo ne a dai dai lokacin da 'yan Nijar da dama suka zura ido suna jiran a gurfanar da hamshaƙin ɗan kasuwar a kan zargin da gwamnatin ta yi masa na yin sama da faɗi da wasu kuɗaɗe sama da biliyan ɗaya da rabi. Abin da ya sa 'yan ƙasar ta Nijar ke azza ayar tamba a kan yunƙuri na shugaban ƙasar na yaƙi da sotar dukiyyar ƙasa. Malam Sumaila Amadu shi ne shugaban jam'yyar PND Ya ce '' Muna jiran mu gani idan gwamnatin da gaske ta ke kan cewar za ta iya hukunta duk wani mutumin da aka samu da laifin yin almudahana''

Tijani Abdulkadiri
Tijjani Abdulkadri wani ɗan majalisar dokokin LumanaHoto: DW/Mahamman Kanta
Sitzung des Parlaments in Niger
'yan majalisun dokokin NijarHoto: DW/M. Kanta

Maratanin jam'yyar PNDS Tarraya a kan batu

Alhaji Zakari Oumaru ɗan majalisar dokokin kana kuma jigo a jam'yyar ta PNDS Tarraya ya ce ba hujja ce ba ta samun kariya ga Zakan sannan ya ƙara da cewar.Ya ce '' A sannin mu Zakai kuɗaden da ake cewar ya yi sama da faɗi da su ya riga ya biya,amma duk da haka a yanzu aikin kotu ne ta bincike shi idan yana da wai laifi.''

Yanzu dai 'yan Nijar sun zura ido su ga yadda batun yaƙi da almundahnar zai kasance a nan gaba a ƙasar ta Nijar.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Gazali Abdu Tassawa
Edita : Abdourahamane Hassane