1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece kuce a kan zaben shugaban kasar Madagaska

October 24, 2013

Bayan tsawon shekaru hudu na kwan gaba kwan baya dangane da batun zaben Madagaska, a wannan Jumma'ar ce al'umma ke jefa kuri'a.

https://p.dw.com/p/1A5p3
GettyImages 185550122 People work at the campaign headquarters of presidential candidate Robinson Jean-Louis in Antananarivo on October 21, 2013 ahead of the elections on October 25, 2013. Absent from Friday's presidential election in Madagascar, the current country's strongman Andry Rajoelina and former President Marc Ravalomanana closely monitor the polls which are also followed by mysterious but generous donors, anxious to defend their local economic positions. The two main protagonists in the Malagasy crisis have their favorites among the 33 candidates. Marc Ravalomanana has dubbed the physician Jean Louis Robinson, while three other candidates come from the TGV, Rajoelina's party. AFP PHOTO / RIJASOLO (Photo credit should read RIJASOLO/AFP/Getty Images)
Hoto: Rijasolo/AFP/Getty Images

Cikin tsawon shekaru hudu ne dai a ke ta kai ruwa rana dangane da batun zaben shugaban kasa a Madagaska, domin zakulo mutumin da zai jagoranci fitar da kasar daga rikicin tattalin arziki da na siyasar da ta tsunduma ciki. Ba wai kawai 'yan kasar ba, a'a, harma da kasashen duniya na cike da fatan gudanar da zaben cikin nasara. Sai dai bisa la'akari da yawan 'yan takarar da ke neman kujerar shugaban kasar, masana harkokin siyasa na kaucewa hasashen mutunen da za su yi nasarar kai wa zagaye na biyu na zaben. Jean Herve Rakotozanany, daya ne daga cikin masu korafi a kan yawan 'yan takarar:

Ya ce " Cikin 'yan takara 33, gaskiya ne babu wasu sanannu a fagen siyasa. Abin da ya bani mamaki shi ne duk da kasancewa ta dan jarida ne na tsawon shekaru 15 zuwa 17, amma cikin 'yan takarar, akwai wadanda ma ban taba jin labarinsu ba."

Opposition leader Andry Rajoelina arrives at a rally in Antananarivo, Madagascar, Tuesday March 17, 2009. Madagascar's president handed over power Tuesday, but not to the rival who plunged this Indian Ocean island nation into weeks of turmoil with his bid for power. In a radio address Tuesday, President Marc Ravalomanana said he was ceding power to the military. (AP Photo/Jerome Delay)
Andry Rajoelina, yayin gangamin kawar da RavalomananaHoto: AP

Tushen rikicin siyasar Madagaska

Wani boren da 'yan kasar suka yi a shekara ta 2009 ne ya kai ga tserewar shugaban kasar a wancan lokacin Marc Ravalomanana zuwa ketare, inda Andry Rajolina kuma ya dare bisa kujerar mulki a matsayin shugaban kasa na wucin gadi. Sai dai kuma takaddama akan rashin dacewar tsayawarsu takara, ta sanya dage zaben shugaban kasar a lokuta daban daban, inda al'ummomin kasa da kasa suka taka rawa wajen tabbatar da ganin cewar, ba su sami damar shiga cikin takarar ba, wanda Jean Herve Rakotozanany, wani dan jarida da ke kasar, ya ce ana yi masa fassara ta daban :

Ya ce "Wasu na cewar, ba zaben 'yan Madagaska ba ne, amma na al'ummomin kasa da kasa domin cimma wani burinsu. Amma tunda zaben shugaban kasa ne, to, kuwa kasa za ta amfana."

Daga can ketare dai tsohon shugaba Ravalomanana yayi kira ga goyon bayan tsohon ministan kula da lafiya a gwamnatinsa, yayin da shi kuwa Rajolina yayi gum da bakinsa saboda kasancewarsa shugaban wucin gadin da ke jagorantar kasar komawa bisa tafarkin dimokradiyya, ko da shi ke kuma kowa ya san cewar, yana goyon bayan ministan kudi a karkashin gwamnatinsa ne wanda ke cikin jerin 'yan takara.

GettyImages 185550303 View of a pamphlet explaining people how to vote as Independent National Electoral Commission for Transition (CENI-T) members set up a polling station in Antananarivo on October 21, 2013 ahead of the elections on October 25, 2013. Absent from Friday's presidential election in Madagascar, the current country's strongman Andry Rajoelina and former President Marc Ravalomanana closely monitor the polls which are also followed by mysterious but generous donors, anxious to defend their local economic positions. The two main protagonists in the Malagasy crisis have their favorites among the 33 candidates. Marc Ravalomanana has dubbed the physician Jean Louis Robinson, while three other candidates come from the TGV, Rajoelina's party. AFP PHOTO / RIJASOLO (Photo credit should read RIJASOLO/AFP/Getty Images)
Sumfurin takardun zabeHoto: Rijasolo/AFP/Getty Images

Makomar sakamakon zaben

A karon farko dai tsarin zaben kasar ya tanadi daukacin sunayen 'yan takara a kan takarda guda, maimakon takardu daban daban, wanda hukumar zaben ta ce na da munufar hana tafka magudi, amma kuma ke shan suka. Sahondra Rabenarivo, wata mai fafutukar kare hakkin jama'a a kasar, ta koka game da jinkiri da matsalolin da ke tattare da zaben, wanda ta ce ka iya ruda masu jefa kuri'a, harma ´take tababa a kan ingancin sakamakonsa:

Ta ce " Babbar ayar tambaya kenan. Muna dai fatan komi ya kammala lafiya, kuma mutane su fito kwansu da kwarkwatansu domin jefa kuri'a, kana ya kasance babu magudi, musamman ma yadda wanda ya sha kaye zai amince da hakan, domin idan ba haka ba, to za a iya samun rigingimu a tsakanin zagaye na farko da na biyu na zaben."

A dai ranar 20 ga watan Disamba ne 'yan takara biyu da suka yi nasarar kasancewa a sahun farko cikin 'yan takarar shugaban kasa 33, za su fafata a zagaye na biyu na zaben Madagaska.

Mawallafi : Müller, Friederike /Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani