1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece-kuce kan nada mata mukamun kantoma

July 20, 2017

Wata muhawara ta turnike sakamakon nada mata kantoma a kananan hukumomi biyu a Jihar Kano da ke Najeriya.

https://p.dw.com/p/2gttq
Nigeria Schiitische Pilger in Kano
Hoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Muhawara na ci gaba da turnukewa a tsakanin malamai da sauran masu fashin baki kan al'amuran da suka shafi al'umma, dangane da batun kin amincewar da majalisar dokokin jihar ta yi na tantance wasu mata da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya nemi a nada su a matsayin shugabannin riko na kananan hukumomin jihar, bisa dalilai na addini da fari dai gwamnan jihar Kano ne ya mika sunayen mutane 36 da yake son nadawa a matsayin kantomomi ciki har da wasu mata guda 2 lamarin da wasu malamai suka yi ta sukar lamirin suna masu cewar hakan ya saba da addini lamarin da ya janyo dole majalisar ta ki amincewa da su, to amma wasu malaman da masu fashin baki na ganin cewar babu wani dalili na addini na hana mata rike mukamai illa dai kawai malaman na kara fito da hanyoyin danne mata.

Parlamentswahl 2011 in Kano State Nigeria
Hoto: DW

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun malamai suna fitar da fatawowin da ke hana mata tsallake wasu iyakoki musamman a tsarin gudanarwar mulki da zamantakewa sai dai kuma a lokuta da dama bakin malaman yakan bambanta da juna dangane da batun bambamcin da ke akwai tsakanin mace da namiji. Yanzu haka dai majalisar dokokin Jihar Kano ta ki tantance sunayen wadannan mata da aka kai domin tantance su a ba su mukamin kantomomi bisa dalilan cewar ya saba da addinin Musulunci. Sai dai kuma masu fashin baki kan lamuran yau da kullum na ganin cewar da fari ma wannan batu tamkar cin fuska ne ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje wanda ake masa lakabin Khadimul Islama tun da dai suna ganin ya yi nazari kafin tura sunan.

Wani abu da shi ma ke jan hankalin mutane shi ne yadda ake burus da batun wasu matan idan za a nada kan shugabanci, alal misali yanzu haka akanta janar ta kano mace ce, baya ga kwmaishinoni da sauran mata da ke rike da mukamai amma hudubobin malaman ba su shafe su ba.