1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta haramta amfani da Nikaf

Abdoulrazak Garba Baba Ani/PAWJune 18, 2015

Wannan matakin dai na cigaba da janyo cece-kuce daga al'ummomin Chadi da kewaye, wadanda ke ganin ba zai magance matsalar ba.

https://p.dw.com/p/1FjHf
Symbolbild Eine Frau trägt Burka
Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin Chadi ta haramta amfani da nikaf, da duk wani abin da zai rufe fuskar mutun a duk fadin kasar. A wani taron da ya hada shi da jami'an gwamnati da na addini, firaministan Chadi Kalzeubet Pahimi Deubet ya isar da wannan sako wanda shugaban kasa Idris Deby Ituno ya bayar. Wannan matakin na zuwa ne bayan da mutane 33 suka hallaka sakamakon wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake, wanda ake zargin kungiyar Boko Haram da kaiwa a makon da ya gabata.

"Daga yau, an dakatarda amfani da nikaf, ba a makarantu ko wuraren da akwai jama'a ba. Wannan doka ta shafi kasar baki daya, duk wani nau'in suturan da ke rufe fuska ya bar idanu a waje, abu ne mai taimakawa wajen fidda kama, kuma an haramta shi daga yanzu."

Wannan sako ne firaminista Pahimi Deubet ya baiwa shugabanin addinin Kirista da na Musulmi wanda ya bukace su sa su bayar a wuraren ibada dan ganin cewa kowa ya bada hadin kai. A yanzu dai an baiwa jami'an tsaro umurnin cewa duk wanda ya taka wana doka, su tabbatar da sun kama shi an kuma yi mi shi shari'ar gaggawa domin a yanke mi shi hukunci.

Dalilin daukar wannan mataki

Tagwayen hare-haren wadanda suka afku ranar litini, su ne na farko na irin wadanda ake zargin kungiyar Boko Haram da kaiwa, wadanda aka taba gani a babban birnin Chadin wato Injamena, tun bayan da kungiyar ta fara kai hare-hare a kauyukan da ke kusa da iyakarta da Najeriya.

Ranar talata gwamnatin Chadi ta kebe kwanaki uku dan zaman makokin wadanda suka hallaka. Shugaba Deby dai ya ce bai yi mamakin wadannan hare-hare ba, bisa la'akari da muhimmiyar rawar da kasarsa ke takawa wajen yaki da wannan kungiya wadda ta addabi Najeriya da makotanta.