Tsamin dangantakar Jamus da Chaina
September 11, 2019Mtakin Chainan dai na zuwa ne bayan da ministan harkokin kasashen ketare na Jamus din Heiko Maas ya gana da shugaban masu zanga-zanga a yankin Hong Kong Joshua Wong a farkon wannan makon. Jakadan Chainan a Jamus Wu Ken ya nunar da cewa Beijing ta bayyana rashin jin dadinta karara, kan ganawar tsakanin Maas da Wong yana mai cewa hakan ka iya janyo baraka a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Dama dai sau da dama mahukuntan Chainan sun bukaci da a hana Wong takardar izinin shiga Jamus din wato visa, sai dai a wannan Larabar Joshua Wong da ke zaman jagoran fafutukar tabbatar da mulkin dimukuradiyya a Hong Kong din, ya halarci wani taron manema labarai a Berlin fadar gwamnatin Jamus, tare da yin kira ga mahukuntan na Berlin da su yi tir da yadda 'yan sanda ke murkushe masu zanga-zangar a yankin na Hong Kong da karfin tuwo.