1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan wasan Najeriya sun kasa fitar da kitse daga wuta

Gazali Abdou Tasawa AMA
October 21, 2019

A cikin shirin na Labarin wasanni za a ji yadda wasu manyan kasashen Afirka a fagen kwallon kafa sun kasa kai bantensu a wasannin cancantar shiga cin kofin Afirka na 'yan wasan da ke bugawa a gida wato CHAN.

https://p.dw.com/p/3RerT
Afrikanische Nationenmeisterschaft 2018 Marokko - Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/F. Senna

A fagen wasan kwallon kafa a karshen makon ne aka buga wasannin karshe na neman cancantar shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka ta 'yan wasan da ke bugawa a gida zalla wato CHAN ta shekara ta 2020 karo na shida wacce kasar Kamaru za ta karbi bakuncinta. Wannan wasa dai ya zo da ba zata inda wasu daga cikin kasashen nahiyar da suka yi fice a fannin kwallon kafa irin su Ghana, Najeriya, Cote d'Ivoire,  suka kasa kai bantensu a wannan karo. Cote d'Ivoire ta sha kasa a gaban Jamhuriyar Nijar wacce ta yi waje rod da ita bayan da ta doke ta da ci biyu da daya a wasanni biyu da suka buga gida da waje. Ita ma kasar Ghana ta kasa kai labari a gaban Burkina Faso wacce ta doke ta ci ci daya da babu a gida bayan da suka yi banza-banza a Ghanar, a yayin da ita kuwa Najeriya ta yi raggon kaya a gaban kasar Togo wacce ta doke hudu da daya a gida a yayin da Najeriya ta doke Togo da ci biyu kadai a wasan kome. A yanzu dai kasashe 16 da suka samu tikitin zuwa gasar ta CHAN sune Kamaru mai masukin baki , sai Jamhuriyar Dimukuradiyyar kwango, da kwango Brazaville, Mali, Guine Togo, Burkina Faso, Nijar Tunusiya Maroko, Zinmbabuwe Zambiya Yuganda, Ruwanda Namibiya Tanzaniya

Fagen wasannin Bundesliga A karshen mako aka buga wasannin mako na takwas. Sai dai kuma sabanin yadda aka saba gani a shekarun baya inda manyan kungiyoyi biyu na kasar ta Jamus Babba Bayern Münich da Karama Borüssia Dortmund ke yin abin da suka ga dama su dama daudawarsu cikin moda su kuma karya inda ba gaba, a shekarar bana Bundesligar na cike da kalubale inda ake fuskantar kare jini biri jini a kusan kowane wasa kamar yadda ta kasance karawarta da Augsburg da ke a matsayin ta 16 a tebirin na Bundesliga da amma ta rike mata wuya aka tashi ba kare bin damo da ci 2-2 inda Bayern Münich ta yi sababulwa ta bar Ausburg farke kwallo ta biyu ana cikin karin lokaci. Ko baya ga kasa cire wa kanta kitse a wuta kungiyar ta Bayern Munich ta kuma yi asarar dan wasanta na baya Niklas Süle a sakamakon raunin da ya ji a gwiwa inda zai share watanni yana jinya a cewar likitoci bayan da aka yi masa aiki a jiya. Da kyar da jibin goshi ne dai ita ma yaya karama ta sha a karawar Borusiyoyi inda ta doke Mönchengladgach da ci daya da babu. Sai dai duk da haka Kungiyar ta Mönchegladbach na ci gaba da zama a saman tebirin na Bundesliga da maki 16. Wolfsburg wacce ta yi kunnan doki na daya da daya da Leipzig a gidanta na a matsayin ta biyu ita ma da maki 16. Bayan Leipzig ta fara zura kwallo a minti na 54 kafin dan wasan gaba da Wolfsburg ya barke kwallo a minti na 82 a wasan da shi ne ma muka gabatar maku da sharhinsa kai tsaye a shirinmu na Bundeliga kai tsaye A Yanzu dai Bayern Münich da Dortmund da kuma Leipzig na daya bayan daya a matsayin na uku da na hudu da na biyar kowannensu da maki 15. 

Fussball-Bundesliga - FC Augsburg vs. Eintracht Frankfurt
Hoto: picture-alliance/Eibner-Pressefoto/Krieger
Bundesliga Borussia Dortmund v Borussia Mönchengladbach
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Kirchner

Gasar zari ruga ta duniya  A gasar cin kofin kwallon zari ruga ko ruguby ta duniya da ke gudana a kasar Japan inda a karshen mako aka buga wasannin kwata Final inda Ingila ta doke Ostareliya da ci 40 da 16, New Zeland ta lallasa Ayland 46-14, Wales ko Pays des Galles ta doke Faransa da ci 20 da 19 a yayin da Afirka ta kudu ta wulakanta mai masaukin baki Japan da ci 26-3 a gaban magoya bayan kimanin dubu 50 a filin wasa na Tokyo Stadium. A karshen wasan Siya Kolizi Captain din 'yan wasan na Afirka ta Kudu ya yi tsokaci a game da nasarar tasu yana mai cewa: "Ya ce mun san cewa mun fi su karfi, amma ba mu samu dama ba har zuwa hutun rabin lokaci. Amma da aka je hutu mun gargadin junanmu kan cewa mu yi hakuri mu ci gaba da wasa kamar yadda muka fara, kuma daga karshe hakurinmu ya biya domin sun yi wasu kurakurai da suka ba mu damar zura kwallaye. Amma a jumulce wasan namu ya yi kyau"

Rugby World Cup | Gerogien vs Uruguay
Hoto: picture-alliance/AP Images/D. Tomita

A wasannin kusa da na karshe Ingila za ta fafata da New Zeland a ranar Asabar mai zuwa a yayin da Wales za ta kece reni da Afirka ta Kudu a ranar Lahadi. A Sahare guda kuma gasar kwallon Tennis ta birnin Anvers na ci gaba da gudana kasar Beljiyam wacce Andy Murray na Birtaniya ya lashe bayan da doke Stanislas Wawrinka na kasar Swiltzerland da ci 3-6, 6-4, 6-4. Wannan dai shi ne kofi na 46 da Andy Murray dan shekaru 32 ya taba lashewa a tarihin wasan kwallon Tennis.