1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen biyu na shirye shiryen tattaunawa a wannan makon

Kamaluddeen SaniNovember 4, 2015

Shugabanin kasashen China da Taiwan na shirye- shiryen gudanar da wata tattaunawa a wannan makon da muke ciki a kasar Singapore kamar dai yadda wata majiya daga dukkanin bangarorin biyu ta nunar a ranar larabar nan.

https://p.dw.com/p/1GzEV
Taiwanischer Präsident Ma Ying Jeou und chinesischer Präsident Xi Jinping
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan tattaunawar dai na kasancewa irin ta farko tun lokacin da bangarorin suka dare biyu bayan yakin basasar kasashen a shekara ta 1949.

Ana saran cewar tattaunawar zata bada wata kafar kara kyautata dangantaka a tsakanin bangarorin biyu tare da samun dai -dai tuwa a tsakanin su.

Kazalika Amirka a nata bangaren na maraba da wannan matakin kana kuma za ta sanya idanu sosai akan tattaunawar da zata gudana a tsakanin Chinan da Taiwan ata cewar fadar White House ta Amirka.