1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta bada tallafi don yaki da Ebola

October 20, 2014

Wadannan kudade dala miliyan shida za a yi amfani da su cikin wani shirin samar da abinci ga kasashen da cutar Ebola ta fi yi wa barna a yammacin nahiyar Afrika.

https://p.dw.com/p/1DYYT
Symbolbild Ebola Westafrika
Hoto: Reuters

Shirin samar da Abincin na Duniya WFP ya bayyana a ranar Litinin dinann cewa; wadannan kudade za a tura su zuwa kasashen Laberiya da Saliyo da Guinea inda Cutar ta Ebola tafi kamari.

Wannan cuta dai a wadannan kasashe ta sanya manoma da dama kauracewa gonakinsu da dabbobinsu ga hauhawar farashin kayan abinci da ma kawo tarnaki ga shirin jigilar kayan abinci daga yanki zuwa yanki.

Wannan kudi ya kuma zama wani bangare na irin tallafin wannan kasa ta China bayan da a baya ta tura maaikata da kayayyakin kula da lafiya ga wadannan kasashe uku.

China ta kasance kasa ta biyu me karfin tattalin arziki da ta bada tallafi mafi girma cikin tallafin kasashen duniya a yaki da wannan cuta ta Ebola.