1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da kai farmaki a kan 'yan IS

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 26, 2014

Amirka da kawayenta na ci gaba da barin wuta a yankunan da ke da arzikin man fetur a kasar Siriya, a kokarin ganin sun shafe babin kungiyar IS ta masu kaifin kishin addini.

https://p.dw.com/p/1DLO1
Hoto: AFP/Getty Images/Brendan Smialowski

Daraktan kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya Rami Abdel Rahman ya ce sojojin da Amirkan ke yiwa jagora sun kai farmaki a yankuna biyu na gabashin gundumar Deir Ezzor da ke da arzikin man fetur. Ya kara da cewa Amirkan da kawayenta sun kuma yi barin wuta a yankin Hasakeh. Kungiyar kare hakkin dan Adam din mai sanya idanu a yakin na Siriya da ke da zama a Birtaniya ta sanar da cewa hare-haren da Amirkan ke jagoranta ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan ta'addan na IS su 140 da kuma fararen hula 13. Sai dai kawo yanzu Amirkan ba ta ce komi ba dangane da mutuwar fararen hular. Kwararru dai na ganin cewa 'yan kungiyar IS na samun kimanin miliyan daya zuwa miliyan uku na kudin Euro a kowace rana sakamakon albarkatun man da suke sayarwa ta barauniyar hanya wanda kuma ake ganin ta wannan hanya ne kungiyar ke samun kudaden da ta ke gudanar da ayyukanta.