1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da rikici a Bangui

November 27, 2016

Kasancewar dakarun MDD a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bai hana tashin hankali da ake yi ba.

https://p.dw.com/p/2TKjJ
Zentralafrikanische Republik Blauhelmsoldat
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A sharhunan jaridun Jamus na wannan mako zamu fara ne da batun rikicin kasar Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, jaridar Neues Deutschland, a labarinta ta ce duk da kasancewar dakarun MDD da ke aikin kiyaye zaman lafiya, amma har yanzu ana ci gaba da kisan mutane. A cewar jaridar dubban yara kanana ne suka shiga aikin soja, kuma har yanzu babu alaman ganin bayan wannan rikicin. Jaridar ta ce Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kasa ta biyu mafi talauci a duniya, yakin basasan da aka yi ya jefa dubban yara kanana cikin hatsari, kuma kawo yanzu ba a daina samun kisan mutane nan da can ba. Ga kuma rashin wadattatun cibiyoyin kiwon lafiya, abin da yasa yara da mata ki mutuwa sanadiyar cututtuka da suke kamuwa da su. 

Ita kuwa jaridar die tageszeitung, ta rubuta labarinta ne kan sanarwar cocin Katolika a kasar Ruwanda. Jaridar ta ce a karon farko cocin Katholika ya amsa cewa akwai hannunsa a kisan kiyashin da ya faru a kasar cikin shekara ta 1994. A taron shekara da cocin ya gudanar, shugabannin sun bayyana cewa ko da yake bawai dukkanin cocin Katholika za a dorawa laifi, amma fa sun amince cewa wasu daga cikin limaman cocin a wancan lokacin, sun yi amfani da lokutan sujjada na ranakun Lahdi da sauransu, don ingiza gyama da kuma jawo kisan 'yan kabilar Tutsi.

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung, ta duba habakar tattalin arzikin kasashen Afirka ne da kuma yadda sauyin yanayi ke shafar kasashen. A yanzu duniya ta fara tunawa da bala'in fari da aka samu a shekarun 1970 izuwa da 80, inda a wancan lokacin aka yi ta ganin iyaye na dauke da yara wadanda tamuwa ta yi wa illa, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kasashen Habasha, Somaliya Najeriya da sauran wasu kasashen yankin Sahel. Ko da yake jarida ta bayyana cewa lallai kam an samu habakar tattalin arziki a yanzu in aka dubi wasu kasashen Afirka kuma matsalar yunwa ta yi sauki matuka, musamman a kasashen da aka samu dorewar siyasa mai inganci, amma fa batun sauyin yanayi yana ci gaba da yin illah, musamman ganin yadda a kasashen Afirka ake samun karuwar jama'a fiye da karuwar da tattalin arzikin kasashen ke yi. 


Sai jaridar die tageszeitung, wace ta duba siyasar kasar Zimbabwe, inda jaridar ta yi sharhi kan sake tsayawar takaran shugaban Zimbabwe Robert Mugabe. Jaridar ta ce a dai-dai lokacin da zaben shugaban kasa da kuma taron babban jam'iyar ZANU PF ke karatowa, a yanzu mahawara ta na kara zafi, kan ko a sake barin Mugabe dan shekaru 92 da haifuwa ya sake yin takara a zaben kasar da ke tafe a shekara ta 2018. Wasu dai na yin kira ga jam'iyar da yanzu yakamata ta sanar da wanda zai gaji Robert Mugabe, mutumin da ke mulkin kasar tun samun 'yancin kai a shekara 1980.