1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da tattauna batun nukiliyar Iran

October 16, 2013

Nan gaba kadan za'a yi wata sabuwar tattaunawa tsakanin manyan kasashen duniya shida da Iran a birnin Geneva na Amirka kan batun makamashin nukiliyar Iran din.

https://p.dw.com/p/1A0pF
Hoto: Reuters

Kasar Iran ta nuna cewa a shirye take ta rage yawan ayyukanta da take gudanarwa a kan mallakar makamashin nukiliya, wanda hakan ke nuni da cewa a kwai yiwuwar su sasanta da kasashen yamma domin rage takunkumin karya tattalin arziki da suka kakaba mata.

Sai dai har ya zuwa yanzu ba a bayyana cikakkun sharuddda ko kuma bukatun da Iran din ta gindaya ba kafin cimma yarjejeniya da manyan kasashen duniya shidda a tattaunawar da suke ci gaba da gudanarawa a birnin Geneva na kasar Amirka.

Ana sa ran nan da makwanni masu zuwa, za a sake tattaunawa kan makamashin nukiliyar Iran din, tsakanin manyan kasashen duniya shida da suka hadar da Amirka da Rasha da China da Faransa da Britaniya da kuma Jamus a Geneva, sai dai kasashen sunce suna taka tsan-tsan kan ko tattaunawarsu da Iran din za ta cimma nasara ko kuma akasin hakan.

Kasashen na yamma dai na zargin Iran da fakewa da shirnta na makamashin nukiliya tana kokarin mallakar makaman kare dangi, zargin da a ko da yaushe Tehran din ke musantawa tana mai cewa shirinta na zaman lafiya ne.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu