1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da zanga zanga a kasar Tunisiya

Carl Richard HolmFebruary 8, 2013

'Yan Tunisiya na shirin gudanar da zanga zangar yin Allah wadarai da kashe Chokri Belaid, a lokacin jana'izar shi madugun 'yan adawan da ya yi fice wajen sukar manufofin gwamnati.

https://p.dw.com/p/17adI
Hoto: AFP/Getty Images

Dubban 'yan Tunisiya ne ake sa ran za su fantsama kan titunan kasar a wannan juma'ar domin gudanar da zanga-zangar yin Allah wadarai da kashe madugun 'yan adawan kasar wato Chokri Belaid. Hadeddiyar kungiyar Kodagon kasar ce ta yi kira da aka gudanar da wannan zanga zangar, a ranar da za a yi jana'izar shi wannan lawya da ya saba sukar manufofin jam'iyar Ennhda da ke mulki.

Jerin zanga-zangogi aka gudanar a Tunis da kuma wasu birane na Tunisiya a ranakun laraba da alhamis, bayan da wani da ba san kowane ne ba ya harbe Chokri Belaid lokacin da ya fito daga gidansa. 'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zanga. Sai dai kuma sun mayar da martani a birnin Gafsa inda suka yi ta harbin 'yan sanda da duwatsu da kuma kulake.

Kusoshin jam'iyar Ennahda da ke mulki sun rabu gida biyu game da matakin da firaministan Tunisiya Hamadi Jebali ya dauka na kafa gwamnati da za ta kunshi kwararru zalla domin kwantar da hankulan al'uma. Jebali ya dauki wannan matakin ne sa'O'i kalilan bayan hallaka Chokri Belaid.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman