1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da zubar da jini a Siriya

December 12, 2012

Ministan cikin gidan Siriya ya tsallake rijiya da baya sa'ilin da wasu bama bamai 3 suka tarwatse a farfajiyar ma'aikar.

https://p.dw.com/p/171NK
Syrian men inspect the scene of a car bomb explosion in Jaramana, a mainly Christian and Druze suburb of Damascus, on November 28, 2012. Simultaneous bombings in the mostly Druze and Christian town of Jaramana near Damascus killed at least 38 people and sent residents fleeing in panic, a watchdog and witnesses said. AFP PHOTO/LOUAI BESHARA (Photo credit should read LOUAI BESHARA/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images

Wasu abubuwan da suka tarwatse - ciki harda bam da aka dasa cikin wata mota a farfajiyar ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Siriya sun janyo mutuwar akalla mutane bakwai, yayin da wasu 50 kuma suka sami rauni. Jami'an tsaron Siriyar da suka sana da hakan a wannan Larabar (12.12.12), suka ce ministan kula da harkokin cikin gidan Siriyar Mohammad al-Shaar, ya tsira daga harin - ba tare da jin rauni ba.

Tunda faro dai kanfanin dilancin labaran Siriya SANA ya ce bama-bamai ukku ne suka fashe a wajen ma'aikatar cikin gidan da ke birnin Damascus ta yankin kudu-maso-yammacin unguwar Kfar Sousa, daya daga ciki kuma a cikin wata mota ce.

A halin da ake ciki kuma kasashe 120 da ake yiwa lakabi da kawayn Siriya sun amince da kawancen 'yan adawar Siriya a matsayin sahihan wakilan al'ummar kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal