1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban bincike kan bacewar jirgin AirAsia

December 29, 2014

Kasashe da dama da suka hadar da Amirka da Jamus da Ostareliya sun kudiri aniyar bada nasu tallafin a aikin binciken wannan jirgi.

https://p.dw.com/p/1EB0D
Suche nach AirAsia Flight QZ8501
Hoto: Reuters

Jirgin saman AirAsia da ya bace a tekun Java ba shi da dangantaka da makomar MH370 na kasar Malesiya da ya bace a watan Maris a cewar Firaministan kasar Ostareliya Tony Abbott a yau Litinin.

Kasar ta Ostareliya da ta jagoranci aikin binciken wannan jirgi na MH370 da ke kan hanyarsa daga Kuala Lampur zuwa Beijing ya bace ne a ranar 8 ga watan Maris da mutane 239 a cikinsa.

Abbott ya ce babban kuskurene ne ma a rika kwatanta bacewar MH370 da wannan jirgi an AirAsia . Ya fadi haka ne a gidan rediyon Sydney 2GB lokacin da aka bayyana bacewar wannan jirgi da fasinjoji 126.

Ya ce wannan jirgi na bisa hanya kuma a lokacin da aka tsara sai dai bacewar na zuwa ne sakamakon gurbacewar yanayi abin da yasa yayo kasa, sabanin na MH370 da kawai ya bace. Shi kuwa na MH17 an harbo shi ne.

Iyalan wadanda ke cikin wannan jirgi dai na ci gaba da zaman jimami da dakon jin wani labari kan makomar 'yan uwansu daga mahukunta.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu