1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban diflomasiyya ga 'yan adawar Siriya

March 26, 2013

'Yan tawayen Siriya sun dare kujerar wakilcin kasar a taron kungiyar Larabawa

https://p.dw.com/p/184SP
Heads of Arab states gather for a group photo during the opening of the Arab League summit in Doha March 26, 2013. A summit of Arab heads of state opened in the Qatari capital Doha on Tuesday expected to focus on the war in Syria as well as on the Israeli-Palestinian conflict. REUTERS/Ahmed Jadallah (QATAR - Tags: POLITICS ROYALS)
Hoto: Reuters

A karon farko, wakilan 'yan adawar Siriya sun hau bisa kujerar wakilcin kasar a lokacin taron kungiyar kasashen Larabawar daya fara gudana - wannan Talatar a daular Qatar, lamarin da ke zama ci gaba ne ta fannin diflomasiyya ga fafutukar da 'yan adawar ke yi na kawar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad. Tawagar 'yan adawar a karkashin jagoracin Mouaz al-Khatib, tsohon shugabanta ta shiga zauren taron ne yayin da ake mata tafi, kana ya zauna a kujerar da kungiyar ta warewa Siriya ne a bisa gayyatar sarkin daular Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani.

Dama tun a makon jiya ne taron ministocin kula da harkokin wajen kasashen Larabawa ya bayar da shawarar mikawa 'yan adawar gurbin kasar ta Siriya a cikin taron. A jawabin daya yi, sarkin na Qatar, mai masaukin baki, ya ce 'yan adawar sun cancanci sabon matsayin bisa karbuwar da suke ci gaba da samu a ciki da wajen kasar ta Siriya.

Idan za'a iya tunawa dai tun a shekara ta 2011 ne kungiyar kasashen Larabawar ta dakatar da wakilcin gwamnatin Siriya a cikin ta bisa abinda ta ce gallazawar da take yiwa masu boren nuna adawa da ita.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou