1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban mahawara kan zaman baƙi a Jamus

October 17, 2010

Shugabar gwamnatin Jamus tace abinda gwamnatin ta za ta sa a gaba, shine tsarin tabbatar da sajewar baƙi 'yan ci rani da jamusawa.

https://p.dw.com/p/PgEX
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, a wani shago sayar da abincin Turkawa.Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabar gwamnatin Jamus Agela Merkel tace samar da al'umma mai al'adu daban daban a ƙasar ta Jamus ya gaza samun nasara. Merkel ta faɗi hakanne a jawabinda ta yi wa ɗinbin matasa daga jam'iyarta ta CDU. Tace dukkan tsare-tsaren da aka yi don samun baƙi su wanzar da rayuwar kafaɗa da kafaɗa tare da jamusawa ya ci tura. 'Yan ƙasar Turkiya dai sune al'ummar da ta fi yawa a ƙasar bayan Jamusawa. Shi ma shugaban ƙasar Turkiya Abdullah Gül ya goyi bayan kalaman Merkel, inda yace duk wani ba turke dake zama a Jamus, to lallai ya koyi Jamusanci, a ji shi rangaɗadau tamkar ba jamushe. Merkel tace babu inda Jamus za ta je ba tare da baƙi ba. Shi ma dai wani ɗan siyasar jam'iyar kare mahalli ta The Green Jügen Trittin, ya buƙaci Jamus ta ƙarfafa gwiwar ƙwararru baƙi 'yan cirani, don su shigo Jamus su bada ta su gudumawar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu.