1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban ziyarar ministan harkokin wajen Jamus a Afirka.

April 8, 2010

Ministan harkokin wajen Jamus ya gana da shugaban Tanzaniya.

https://p.dw.com/p/MqXc
Guido Westerweele, da Dirk Niebel, yayin da suke jawabi a birnin Daressalam na Tanzaniya.Hoto: picture alliance/dpa

A matsayin matakin farko na rangadin da yake yi a Afirka ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle, ya gana da shugaban Tanzaniya, Jakaya Kikwete. Wannan shi ne karon farko da wani ministan harkokin wajen Jamus ya kai ziyara a Tanzaniya cikin shekaru 15 da suka gabata. Westerwelle, na wannan rangadi ne tare da Dirk Niebel, ministan raya ƙasashe masu tasowa. Tuni ya kai ziyarar gani da ido akan shirye-shiryen ba da agaji da ke samun tallafin kuɗi daga Jamus. Ƙasar Jamus dai ta fi mai da hankali ne ga Tanzaniya a shirinta na ba da taimako. A yau ne kuma ministocin biyu za su zarce zuwa Afirka ta Kudu kafin su kammala rangadin nasu a ƙasar Djibouti a ƙarshen wannan mako. A jiya ne ministocin biyu suka fara wannan ziyara ua AFrika inda za su mai da hankali ga bukatar karfafa dangantakar tattalin arziki da shirin ba da taimakon raya kasashe da kuma yaki da talauci ta ba taimako wajen ba horon sana'a ga matasa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu