1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaba da bincike kan badakalar cin hanci a FIFA

Abdourahmane Hassane/Ahmed SalisuMay 28, 2015

Hukumomin shari'a a Amirka na cigaba da kame shugabannin FIFA da ma gudanar da bincike kan badakalar cin hanci da rashawa da ake zargin wasu jami'an hukumar na da, da na yanzu da yi.

https://p.dw.com/p/1FXlv
Schweiz FIFA Schriftzug Hauptquartier in Zürich
Hoto: Reuters/R. Sprich

Sabbin bayanai da suka fito daga ofishin ministan sharia na Amirka a kan wannan badakala sun ce wasu daga cikin shugabannin kungiyar ta FIFA sun karbi na goro har kusan dalla amirka dubu 40 a cikin wani otal makwannin kadan kafin zaben shugaban hukumar a shekarun 2011.

Hukumomin shari'a na Amirka sun ce a cikin shekaru 24 shugabannin kungiyar sun azurta kansu da kudaden kungiyar ba kan ka'ida ba da kuma karba cin hanci da rashawa tare da halita kudin haram.

Ya zuwa yanzu jamian kungiyar a kalla guda tara ne kotun ta Amirka ta zarga da laifin karbar cin hanci. a baya bayan nan shi da aka kama da wannan laifi da ake zargin su da shi shi ne tsohon mataimakin shugaban hukumar FIFA din Jack Warner ko da dai mutummin ya musanta wannan zargi da ake masa.

Wannan hali da ake ciki dai ya sanya mutane da dama nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda aka tafiyar da hukumar a baya har ma wasu hukumomi na kula da kwallon kafa kamar UEFA ga misali suka bukaci da a dakatar da zaben sabon shugaban kungiyar da nufin yin bincike don rarrabe tsaki da tsaba.

Jack Warner
Tsohon mataimakin shugaban FIFA Jack Warner na daga wanda aka kama a baya-bayan nan kan zargin cin hanci.Hoto: Getty Images/AFP/L. Acosta
FIFA Sepp Blatter
Shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter na yunkuri na samun wani sabon wa'adi.Hoto: picture-alliance/epa/E. Leanza